Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a ranar Litinin ya sanar da ƙirƙiro da ƙarin manyan masarautu bakwai, jihar yanzu tana da manyan masarautu 14 kenan.
Hakan ya rage wa Lamiɗon Adamawa, Mustapha Barkindo, yanki daga ƙananan hukumomi takwas zuwa huɗu – Yola ta Kudu, Yola ta Arewa, Girei da Hong.
Sabuwar dokar kuma tana nufin Sarkin Mubi, Abubakar Isa-Ahmadu, yanzu yana da ƙananan hukumomi biyu a masarautarsa - Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu, daga biyar.
Masarautun Adamawa da Mubi, masarautu ne da mafi yawan mutanenta Fulani.
Sabbin masarautun sun haɗa da masarautar Huba, mai hedikwata a Hong mai daraja ta biyu; Masarautar Madagali, mai hedikwata a Gulak da, babban sarki mai daraja ta biyu; da masarautar Michika l, mai hedkwata a Michika mai daraja ta biyu.
Sauran su ne Masarautar Fufore, mai hedikwata a Fufore mai daraja ta biyu; Masarautar Gombi, mai hedikwata a Gombi kuma mai mulki mai daraja ta uku; Masarautar Yungur, mai hedikwata a Dumne kuma mai daraja ta uku; da Maiha Emirate, mai hedikwata a Maiha kuma mai daraja ta uku.
