Fita yin rajistar katin zaɓe na da muhimmanci a jiharmu Kano – Hon. Sunusi Surajo

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An bayyana cigaba da ake samu a zuwan gwamnatin Kano ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa bayyane suke ba a ɓoye ba. 

Mai bai wa Gwamnan Kano shawara akan harkokin siyasa, Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ne ya bayyana hakan.

Ya ce cikin shekara biyu ‘yan fansho na amfana, masu albashi ma’aikata ranar  22 zuwa 23  ga wata ake soma biyan albashi su samu kuɗinsu ba tare da sassaƙa ko zaftara ba.

Ya ƙara da cewa ga ɗaukar ma’aikata da aka yi da tura ɗalibai makarantu a ciki da wajen ƙasar nan aka kuma buɗe manyan makarantu na koyon sana’o’i da aka rufe shekara 8 a gwamnatin Ganduje. Daga irin cigaban da aka samu akwai gyara makarantu da auren gata da sauran aikace-aikace da ake ta gudanarwa da gwamna shi kansa ba zai iya lissafa su  ba a lokaci guda.

Game da masu cewa gwamnatin ta gaza Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ya ce shi maƙiyi ko ruwa ka shiga zai ce ka  tayar da ƙura ne, saboda haka kashin kaji ko’ina yake sai a ɗebo a yaɓa maka, amma wanda ake faɗawa shi mai hankali ya san abinda akayi kuma Duniya ta sani duk abinda ake yi na alheri a wannan gwamnati idan wasu masharranta sun shiga ɗaki sun ƙulla  sharri komai daɗewa gaskiya za ta bayyana.

Ya yi nuni da cewa ba su san da wasu ‘yan adawa da suke cikin gwamnati suke leƙen asiri ba, kuma su tafiyarsu tsarkakkiya ce a Kano, hanya ɗaya ce kuma duk wanda yake Kwankwaso da kwankwasiyya  da Injiniya Abba Kabir Yusuf baya  tunanin yin abinda bai kamata ba, tafiya ake cif da cif tsaf.Jam’iyyasu ta NNPP me Littafi da hular digiri mai  ja da fari a haka ake jajircewa ake aiki tuƙuru ana ɗaukaka ilimi da koyar da tarbiyya.

Ya ce masu adawa da Kwankwaso tun ba a shiga NNPP ba wane irin surutu ne PDP ba ta yi ba cewa Kwankwaso zai bar PDP ya koma APC haka APC ta yi ta cewa zai dawo APC amma ya kafa DNM daga nan ya shiga NNPP. Saboda idan mutum ya riƙa kowa idan yaci abinci ya miƙe ƙafa sai ya faɗi abinda yake so.Amma koma menene lokaci ne zai nuna, amma yanzu  Kwankwaso yana nan a NNPP da ita suka shiga zaɓe suka ci.

Hon. Sunusi Surajo yace masu yin ƙorafi  a ce wai  mutumin da yake jihar Ribas yake Kwankwasiyya ya ce an manta da shi bai yarda da wannan ba, domin shi ya yi wakilci zuwa  jihar Ribas kuma mutane daga Ribas daban-daban sun zo da kokensu an share musu hawaye.

Ya ce idan mutum yasan siyasa yana yinta,zancen ma baka da Gwamnati a Ribas ka ce Kwankwasiyya ta manta da kai kamar ka yaudari kai ne in a Ribas kake Kwankwasiyya, bama can ba duk ƙasarnan duk abinda ya sami ɗan kwankwasiyya,kwankwaso na takawa da kansa yaje  ya nema musu haƙƙi  har Ribas Kwankwaso ya je nema musu haƙƙi, wannan ta basu darajar zama su miƙe ƙafarsu.

Mai bai wa Gwamnan jihar Kano shawara akan harkokin siyasa ya ce abinda ya sa ake zaɓar gwamnati shine ta yi aiki da mutane za su amfana, ba lallai sai kai kaɗai an amfanar da kai ba, wanda yasan siyasa baya ƙorafi na cewar ya wahalta ba a kula shi ba, ya tabbatar yan Kwankwasiyya na jihar Ribas sun zo ya taimaka musu, kuma suna zuwa wajen waɗansu irinsa,in ka gamu da mutum kaji  ya ce dakai  yana Ribas ba a taimake shi ba, ko shine shugaban matasa su ba su ji daga bakinsu ba, kuma  sun san ɗan Kwankwasiyya ba zai yi wannan kalmar ba, duk inda yake in dai Kwankwasiyya yake da gaske.

Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso ya yi kira ga al’ummar jihar Kano gaba ɗaya ba tare da bambanci ba, su fita su yanki katin rijista na zaɓe, wanda ba shi da ita da wanda nasa ya ɓata ya gyara Jihar Kano da ake da yawan al’umma fiye da kowa a ƙasar nan bai kamata a mayar damu baya ba,yakamata mu fita mu jawo hankalin mutane su yi ƙoƙarin karɓa don za ta kai wata ran ko tafiya za ka yi zuwa wani waje, ko wani abu ya zo na ƙaruwa a ce sai an ga katin zaɓenka domin da katin zaɓe dana yan ƙasa suna da muhimmaci mutane su dage suyi.

By ukarofi