Fitaccen jarumin Kannywood, Baba Karƙuzu ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A yammacin yau ne fitaccen jarumin Kannywood, Malam Abdu Kano da aka fi sani da Baba Karƙuzu, ya rasu.

Za a yi masa sallar jana’iza a gobe da safe a gidansa da ke Haruna Hadeja Street, a Jos Babban Birnin Jihar Filato.

Allah Ya jiƙan sa Ya kuma gafarta masa tare da bai wa ƴan uwa da abokan arziƙi haƙurin juriyan rashin sa.

By Babaji