(Ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
A taƙaice dai sauya addini a cikin al’ummar Yarbawa bai zama abin faɗi ba ko bada labari ba, kuma kaso mai yawa daga cikinsu suna canza addinin ne zuwa inda ya fi masu sauƙi ba wai gano gaskiya ba.
Ba wai ina nufin al’ummar Yarbawa ba sa riƙo da addini ba, a binciken da aka yi a kwanakin baya ya nuna yadda bayaraben da ya yi riƙo da addini ke zarce kowa wurin iya yi masa sadaukarwa.
Akan samu wasu ƙalilan daga Yarbawan da suka ƙiya wa wannan al’ada tasu ta fifita al’ada fiye da addini, wanda hakan ke sa da wuya ka samu wani daga cikin iyalansu da zai canza zuwa wani. Domin sun koya wa iyalansu addinin, sun sanar da su ma’anarsa da dalilan da suka tabattar sun gamsar da su kan bin addinin. Wannan yana taimaka wa matuƙa a kan yadda suke kallon wani addinin, kuma zai hane su da sauya shi ba tare da wani babban dalili da ya fi wanda suka taso da shi ba.
A Musulunci, aƙida ba wata al’ada ba ce da mutum yake gada kawai saboda an haife shi a cikinta ba. Ba kuma wani ɓangare ne na rayuwa da za a iya sauyawa saboda tasirin muhalli ko ra’ayin jama’a ba. Aƙida ita ce tushen dangantakar bawa da Ubangijinsa, kuma ita ce ginshiƙin da sauran rayuwarsa take doruwa a kai.
Saboda haka ne Alƙur’ani ya yi magana game da muhimmancin tsayuwa a kan gaskiyar da mutum ya sani. Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa: “Duk wanda ya yi riƙo da wani addini ba Musulunci ba, ba za a karɓa daga gare shi ba, kuma a lahira yana daga cikin masu hasara.” Malamai sun daɗe suna bayanin wannan aya a matsayin tunatarwa game da girman ni’imar shiriya da kuma muhimmancin riƙe gaskiyar da Allah Ya nuna wa mutum.
Haka kuma Annabi Muhammad (SAW), wanda Allah Ya bai wa baiwar imani da shiriya, ya kasance yana yawaita addu’ar cewa: “Ya Mai juya zukata, Ka tabbatar da zuciyata a kan addininka.” Malamai sun ce idan har Manzon Allah yana roƙon tabbatuwa a kan gaskiya, hakan yana nuna cewa babu wani bawa da ya kamata ya ji ya wadatu daga neman taimakon Allah wajen kare imaninsa.
Abin lura shi ne, a duka dalilan da waɗannan mutane da suka yi ridda suka bayar na barin addinin Musulunci, ba wanda ya mayar da hanakali kan shi karan kansa addinin Musuluncin, wato inda ya gaza ko inda suka gane cewa ba shi ne hanyar gaskiya ba. Wasu daga cikinsu sun yi magana ne kan irin tarbiyyar da suka samo a ƙurciya, wasu kuwa sun danganta lamarin da rashin fahimtar wasu abubuwa da suka shafi addinin, yayin da wasu suka ce bincike da nazarin da suka yi da kansu ne ya kai su ga sabon zaɓin da suka yi. Wannan ne zai tabbatarwa mai karatu dukansu sun yi hukunci ne daidai da abinda ya shafi rayuwarsu ba shi karan kansa addinin ba, domin akwai bambanci tsakanin addini da yadda mabiyansa ke wakiltar sa.
Iyaye na iya kuskure, malamai ma na iya kuskure, al’umma ma na iya kasa nuna kyakyawar fuskar addini. Hakan ba yana nufin kuskuren mutane zai iya zama hujja akan gaskiyar addinin da suke bi ba.
Wannan batu ne da malamai suka jima suna jaddadawa a duk lokacin da aka bijiro da zancen dalilan da ke sa wasu mutane su nisanta kansu da addini.
