Daga AISHA ASAS
A Najeriya, addini ba kawai wata al’ada ba ce ko wani ɓangare na rayuwar yau da kullum. Wani ginshiƙi ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen gina mutumtaka, al’adu da yadda jama’a ke kallon mutum. Wannan dalili ne ya sa duk wani canjin addini da ya shafi fitattun mutane ke zama abin jan hankali da muhawara cikin al’umma.
A masana’antar nishaɗi ta Najeriya, inda rayuwar fitattun mutane ke ƙarƙashin hasken jama’a a kowane lokaci, sauya addini na ɗaya daga cikin batutuwan da kan tayar da ƙura. Yayin da da dama daga cikin mashahuran mutane ke ci gaba da bin addinin da aka haife su a cikinsa, wasu sun zaɓi wata sabuwar hanya ta addini, lamarin da ya haifar da tattaunawa mai faɗi a kafafen sada zumunta da ma waɗanda aka sani kafin zuwan na zamani.
Sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci ko kuma akasin haka ba abu ne mai sauƙi ba, musamman ga fitattun mutane da ke rayuwa a gaban idon duniya. Irin waɗannan matakai kan zo tare da tambayoyi daga magoya baya, matsin lamba daga iyalai da kuma muhawarar jama’a a ƙasar da addini ke da tasiri mai zurfi kamar Najeriya. Musamman ma da cewa ba kasafai ba ne ake samun wani daga al’ummar Musulmi ya koma wani ɓangare na wasu addinai ba.
Duk da cewa ga mutane da yawa addini tafiya ce ta kai da kai tsakanin mutum da Ubangijinsa, zamanin kafafen sada zumunta ya sa kusan kowane mataki na rayuwa ya zama abin sharhi da fassara daga jama’a. Wannan ya sa sau da dama magoya baya da masu suka ke saurin yin tsokaci kan duk wani abu da ya shafi rayuwar mashahurai.
A cikin shekarun baya-bayan nan, wasu daga cikin fitattun ’yan Najeriya sun fito fili suna bayyana yadda suka sauya daga Musulunci zuwa Kiristanci, tare da bayyana dalilan da suka kai su ga irin wannan muhimmiyar shawara.
Peller:
“Ni ba Musulmi ba ne, Ina zuwa coci sosai”
Shahararren tauraron TikTok, Habeeb Hamzat wanda aka fi sani da Peller, ya jawo hankalin jama’a a watan Yulin shekarar 2025 lokacin da ya yi bayani game da addininsa yayin wata tattaunawa kai tsaye da mabiyansa.
Peller ya bayyana cewa, duk da sunansa da asalinsa, ba ya kallon kansa a matsayin Musulmi. Ya ce ya daina bin addinin tun yana ƙarami.
Da yake mayar da martani ga masu tambayar addininsa, ya ce: “Me ya sa kuke kirana Musulmi? Ni ba Musulmi ba ne. Ina zuwa coci sosai.”
Peller ya bayyana cewa, wasu abubuwan da ya fuskanta a makarantar allo lokacin ƙuruciyarsa ne suka sa ya fara nesanta kansa da tsarin karatun addinin Musulunci. A cewarsa, tsananin hukuncin da ake yi masa ya bar masa wani raɗaɗi da ya sa daga ƙarshe ya daina zuwa makarantar gaba ɗaya.
Ya ce, daga baya ya samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya a cikin Kiristanci, inda ya bayyana cewa zuwa coci ya ba shi wata sabuwar ma’ana ta kasancewa cikin al’umma da kuma gamsuwar ruhaniya.
Adewale Ayuba:
“Na gaza fahimtar Larabci shi ya sa na nemi hanyar da zan yi magana da Ubangiji kai taye”
Fitaccen mawakin Fuji, Adewale Ayuba, ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da suka haifar da muhawara bayan ya bayyana cewa ya rungumi Kiristanci bayan ya shafe shekaru yana Musulunci.
A matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan taurarin kiɗan Fuji, wanda tarihi ya danganta da al’adun Musulunci, matakin da ya ɗauka ya ja hankalin jama’a sosai.
Ayuba ya bayyana cewa, ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ya fuskanta a lokacin da yake Musulmi shi ne rashin fahimtar harshen Larabci, wanda ake amfani da shi wajen addu’o’i da karatun addini.
Ya ce, sauyin addinin nasa ba shi da alaƙa da batun aure ko iyali. A cewarsa, tun yana Musulmi bai taɓa ganin cewa auren mata da yawa wajibi ne ga kowane Musulmi ba.
Mawakin ya ce: “Lokacin da nake Musulmi ban kasance mai yawan mata ba. Na kasance tare da matata. Wasu suna cewa Musulmi dole ya auri mata da yawa, amma ni ban ga hakan a cikin Alƙur’ani ba. Matsalata ita ce, ban fahimci Larabci ba, kuma na gaji da ganin wasu ne ke yi min addu’a a koyaushe. Amma da littafi Mlmai tsarki zan iya magana da Allah kai tsaye. Kuma lokacin da na karanta cewa Yesu ya mutu saboda ni, hakan ya ishe ni. Ba kowa ne zai mutu saboda wani ba. Ya yi hakan, kuma shi mai nasara ne. Wannan ne ya sa na zaɓi Almasihu.”
Sai dai ya jaddada cewa addini lamari ne na sirri, yana mai cewa ba ya son shiga doguwar muhawara saboda mutane kan iya karkatar da maganarsa.

Korede Bello:
“An haife ni a cikin Musulunci, amma na kamu da bibiyar littafin Bible da kaina”
Shahararren mawaki, Korede Bello, shi ma yana cikin fitattun ’yan Najeriya da suka fito fili suna magana kan yadda suka sauya addini.
A farkon shekarar 2026, tsohon tauraron Maɓin Records ya bayyana cewa, an haife shi kuma aka raine shi a gidan Musulmi, amma tafiyarsa ta ruhaniya ta kai shi ga rungumar Kiristanci.
A cewarsa, ba wani ya matsa masa lamba ba. Maimakon haka, bincike da nazarin Littafi Mai Tsarki da ya yi da kansa ne suka sa ya yanke wannan shawara.
Ya ce: “Ba a haife ni Kirista ba. An haife ni Musulmi. Sai da na fara nazarin littafi mai tsarki da kaina, ba saboda dalilan addini ba, amma saboda wasu dalilai na kashin kai.”
Da yake hasashen cewa wasu za su soki matakinsa, ya ƙara da cewa: “Kafin ku gicciye ni, ku sani cewa ni Kirista ne, kuma Almasihu ya riga ya mutu saboda ni. An riga an gicciye shi, don haka babu buƙatar hakan a sake.”
Maganganunsa sun samu karɓuwa daga wasu magoya baya da suka bayyana cewa sauyin nasa ya samo asali ne daga bincike, fahimta da kuma ƙoƙarin zurfafa dangantakarsa da Allah.

Tobi Bakre:
Jarumin da ya taso a gidan Musulunci kuma aka shaide shi da zama Kirista
Fitaccen ɗan wasan Nollywood kuma tsohon ɗan takarar Big Brother Naija, Tobi Bakre, yana daga cikin mashahuran Najeriya da suka fito daga gidan Musulmi.
Tobi, wanda ya yi fice bayan fitowarsa a gasar Big Brother Naija ta shekarar 2018, ɗan asalin Jihar Ogun ne kuma ya kammala karatu a Jami’ar Legas.
Duk da cewa rahotanni sun danganta shi da asalin Musulunci, a yau an fi ganinsa a cikin al’ummar Kirista, musamman saboda yadda yake bayyana bangaskiyarsa a fili tare da iyalinsa.
Ya kasance ɗan gidan fitaccen ɗan kasuwa kuma shugaban banki, Chief Olufemi Bakre, yayin da ya samu karɓuwa sosai a masana’antar fina-finan Najeriya bayan sauya sheƙa daga duniyar talabijin zuwa harkar fim.

Sola Allyson:
Daga Rasheedat zuwa shahararriyar mawaƙiyar waƙoƙin Gospel
Shahararriyar mawaƙiyar waƙoƙin bishara, Sola Allyson, ta bayyana cewa tafiyarta ta ruhaniya ta samo asali ne daga bincike da sauye-sauyen rayuwa.
An haife ta cikin gidan Musulmi, kuma sunanta na farko Rasheedat ne. Mahaifinta ma Musulmi ne, kuma an raineta cikin koyarwar Musulunci kafin daga baya ta fara kusantar Kiristanci.
A cewarta, lokacin da ta koma zama a Ikorodu tare da kakanninta ta haɗu da wata tsohuwar ƙawarta wadda ta fara kai ta coci. Wannan ne ya zama matakin farko na tafiyarta zuwa sabon addinin.
Da take tuna baya, ta ce: “Lokacin da na koma Ikorodu wajen kakannin mahaifina, na haɗu da wata tsohuwar ƙawa ta. Ina bin ta zuwa cocinsu. Kun san an haife ni Musulma. Mahaifina Musulmi ne. Sunana Rasheedat. Ban taɓa ɓoye hakan ba.”
A yau, Sola Allyson tana daga cikin fitattun mawaƙan gospel na Najeriya, inda waƙoƙinta suka shahara wajen isar da saƙonnin bangaskiya, ƙauna da kusantar Allah.
Abin tambayar anan dai shine, mene ne waɗannan fitattun taurari na daga jarumai, mawaƙa da kuma shahararrun ’yan kafafen sada zumunta suke da shi na dangantaka, waɗanda za mu iya samo dangantakar da ke tsakanin shahara da canza addini?
Wannan zai zama darasin da za mu tattauna a mako mai zuwa da yardar Allah.

