
Daga BELLO A BABAJI
Kwamitin shugaban ƙasa kan sayar da ɗanye da tataccen mai ya ce matatar mai ta kamfanin Ɗangote za ta sayar da mai ne kaɗai ga Kanfanin man fetur na ƙasa, NNPCL.
Mamban kwamitin kuma shugaban Hukumar Tattara kuɗin Haraji ta Ƙasa (FIRS), Zacch Adedeji ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja yayin da ake shirin fitar da ɗibar farko ta matatar a ranar Lahadi, 15 ga watan Satumba.
Ya ce, kawo yanzu an cimma yarjejeniya tsakanin bangarorin biyu inda NNPC ke shirin karɓar zangon farko a ranar Lahadi kamar yadda ya sanar a baya.
Ya kuma ce, daga ranar 1 ga watan Oktoba ne NNPC zai fara sayar wa da matatar Ɗangote ɗanyen mai ta hanyar biya da Naira wanda a sakamakon haka ne matatar za ta ke bada fetur da gas na dai-dai darajar abin da ta karɓa daga kamfanin.
“A halin yanzu, za a ke sayar da fetur wa NNPC ne kaɗai. NNPC kuma zai ke sayar wa ƴan kasuwa masu yawa”, inji shi.
Baya ga haka ne, Ministan Kuɗi da na Tattali, Wale Edun ya tabbatar da jawabin tare da yin karin haske, ya na mai cewa ƴan kasuwa masu muradin sayan man, za su saya ne daga NNPC ta hannun kamfanin kasuwancinsa.
Ya ce, wannan wani ɓangare ne na yarjejeniyar da aka ƙulla da hukumar gudanarwa ta matatar Ɗangote kan ƙa’idodin ba ta ɗanyen man da kuma karɓar tataccen daga gare ta.
Sai dai, wannan mataki ya ci karo da iƙirarin da NNPCL ya yi a farkon wannan watan na cewa bai da nufin zama mafi rinjayen mai raba fetur ɗin da matar za ta ke fitarwa.
