Gadauniyar Rabi Gwamna ta gudanar da taron shan ruwa a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gidauniyar bada tallafi ta Rabi Gwamna Charity Foundation ta shirya taron shan ruwa ga mambobin ƙungiya da ‘yan uwa da abokan arziki domin sada zumunci da ya gudana ranar Asabar a Primary Janbulo da ke Kano.

Da ta ke jawabi yayin shan ruwan, Hajiya Rabi Gwamna ta ce sun shirya taron shan ruwan ne don sada zumunci da haɗa kan ƴan ƙungiya don samun lada a wannan wata.

Ta ƙara da cewa “A cikin shekaru 9 da kafuwar wannan Gidauniyar ta tallafawa alummomi a fannoni daban-daban na rayuwa, kamar tallafawa marayu, harkar ilimi, harkar lafiya da sauransu.

“Nasarorin da muka samu a wannan ƙungiya ba zai lissafu ba, kaɗan daga cikin muhimmai akwai samar wa da wata mata da mijinta ya gudu ya barta muhalli, mun yi gini a unguwar Aisami da Gaida, mun yi ginin makaranta, akwai yara da muka kai makaranta, kuma duk shekara muke biya masu ƙudin makaranta, mun biya wa ƴan jami’a kuɗin makaranta, mun ɗinka kayan makaranta guda 100 mun rabawa mabuƙata da sauransu” in ji Hajiya Rabi Gwanna

Sannan ta yi kira ga hukumomi da masu hannu da su tallafawa al’umma don samun rabo a wannan wata na Ramadan mai alfarma.

Taron shan ruwan wanda shi ne karo na biyu ya samu halartar tsohon shugaban marubuta ta ANA kuma shugaban Gidauniyar Kwandala Foundation, da yan Jarida da sauran manyan baƙi maza da mata.