Ganduje ya bada hutun sabuwar Shekarar Musulunci

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ayyana Litinin, 1 ga Muharram, 1443 AH daidai da 9 ga Satumban 2021, a matsayin ranar hutun sabuwar Shekarar Musulunci a jihar.

Sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba, ya sanya wa hannu ta bayyana cewa hutun ya kasance ne don bikin sabuwar shekarar Musulunci ta 1443 AH.

Gwamnan ya buƙaci ma’aikata da su yi amfani da ranar don yin addu’o’i ga jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya don kuɓuta daga matsalolin tsaro da ke fuskanta.

Gwamna Ganduje ya kuma taya al’ummar Musulmi murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci, wacce ke buƙatar nuna godiya ga Allah .

Sanarwar ta ƙara da neman goyon baya da haɗin kai na jama’a ga gwamnati yayin da take yin bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta cika ƙudurorinta ga ‘yan ƙasa a daidai lokacin da ƙasa ke fama da ƙalubalen tsaro.