Gobe Saudiyya za ta fara karɓar neman izinin Umurah daga ƙasashen waje

Fobe Litinin ƙasar Saudiyya za ta fara karɓar neman izinin yin Umurah daga ƙasashen waje, inda za ta fara da adadin alhazai 60,000 kuma za ta kasa ranar yin aikin zuwa lokuta 8, inda zai kai adadin alhazai miliyan biyu a wata.

Kamfanin Dillancin Labarai na Saudiyya ya ruwaito a jiya Asabar cewa Saudiyya za ta fara karɓar neman izinin yin Umurah daki-daki daga gobe Litinin, 9 ga watan Agusta, inda za ta soma da adadin alhazai 60,000.

Kusan shekara ɗaya da rabi kenan da hukumomi a Saudiyya suka dakatar da zuwan alhazai ‘yan ƙasashen waje sakamakon annobar korona da ta mamaye duniya.

Sai dai a bara, ƙasar ta sake buɗe hanyar gabatar da Umurah ɗin amma ga mazauna cikin ƙasar kaɗai.

Mataimakin Ministan Hajji da Umuarah, Abdul-Fattah bin Suleiman Mashat, ya bayyana cewa waɗanda za su nemi iznin yin Umurah sai sun nuna takardar shaidar yin allurar rigakafin korona kafin a ba su.