Kwalara ta kashe mutum 60 a Katsina

Aƙalla mutum 60 ne aka ruwaito sun rasu sakamakon ɓarkewar cutar amai da gudawa ko kuma kwalara, a tsakanin wasu ƙauyukan jihar Katsina.

Kwamishinan lafiya na jihar, Yakubu Danja ne ya bayyana haka ranar Asabar da ta gabata a wajen taron shekara-shekara na 2021 na Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa (NMA) reshen jihar da ya gudana a jihar.

Sai dai, Kwamishinan bai yi ƙarin bayani ba kan takamammen lokacin da aka samu rashe-rashen ba.

Danja ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki matakin gudanar da shirin wayar da kan ‘yan jihar dangane da yaƙi da cutar a tsakanin ƙananan hukumomi 34 da jihar ke da su da zimmar daƙile yaɗuwar cutar.

Ya ƙara da cewa, tuni gwamnati ta sayo magungunan da suka dace na yaƙi da cuta domin raba wa asibitoci a sassan jihar.

Ya ce, “Muna sane da ɓarkewar cutar amai da gudawa da ta addabi wasu sassan jihar, gwamnati na nan na ƙoƙarin ganin yadda za a shawo kan cutar.”

Ya ci gaba da cewa, “A matsayin wani mataki na yaƙi da cutar, gwamnati ta saye magunguna da za ta rabar kyauta don kulawa da waɗanda suka harbu da cutar.

“A halin da ake ciki, an tabbatar da sama da mutum 1,400 sun kamu da cutar a faɗin jihar, sannan sama da mutum 60 sun mutu sakamakon cutar.

“Bari in yi amfani da wannan dama in sanar da al’ummar jihar cewa, cutar amai da gudawa, cuta ce wadda ake iya kare kai daga kamuwa da ita.”

Don haka ya yi kira ga ɗaukacin jama’ar jihar da su zamo masu kula da dukkan matakan da suka dace, kamar lula da tsafta da sauransu, don kariya daga kamuwa da cutar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *