Ganduje ya naɗa Farfesa Jega a matsayin Shugaban Gudanarwar Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa tsohon shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zamanta ta Ƙasa (INEC), Farfesa Attahiru Jega, a matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwar Sa’adatu Rimi dake Kano.

Hakan na cikin wata sanarwa ce da Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Kwamared Muhammad Garba ya fitar.

Sanarwa ta ce Gwamna Ganduje ya kuma amince da naɗin Oba Dakta Sanata Moshood Olalekan Ishola Balogun na Aliiwo a matsayin Babban uba kuma shugaban Kwamitin Gudanarwar Jami’ar ta Sa’adatu Rimi.

A cewar Muhammed Garba, sauran mambobin kwamitin gudanarwar Jami’ar sun haɗa da: Dakta Muhammad Adamu Kwankwaso, Hajiya Zulaiha UM Ahmed, Dakta Ibrahim Yakubu Wunti, Dakta Halima Muhammad da kuma Alhaji Sabi’u Bako.

Idan za a iya tunawa kwanakin baya ne dai Hukumar Kula da Jami’o’i ta Nijeriya, NUC, ta amince da ɗaga likafar Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi zuwa Jami’a.