Gargaɗin EFCC ga ƙungiyoyi kan tallafa wa ta’addanci a ɓoye

Spread the love

A wani mataki na ƙara ƙarfafa yaƙi da ta’addanci a Nijeriya, Shugaban Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon ƙasa da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), Ola Olukoyede, ya gargaɗi ƙungiyoyin sa-kai (NPOs) da su yi taka-tsantsan da yiwuwar shigar ‘yan ta’adda cikin harkokinsu domin amfani da su wajen ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci.

An bayyana wannan gargaɗi ne a yayin ƙaddamar da rahoton tantance haɗarin samar da kuɗaɗen ta’addanci a tsakanin ƙungiyoyin sa-kai (NTFRA) da aka gudanar a Abuja.

Shugaban hukumar ya jaddada muhimmiyar rawar da waɗannan ƙungiyoyi ke takawa wajen tallafa wa jama’a, musamman a fannoni kamar agaji, ilimi da lafiya, amma ya ce wajibi ne a kare sahihancinsu domin kiyaye tsaron ƙasa da kuma amincewar jama’a.

Ya bayyana cewa wannan bincike zai taimaka wajen fahimtar yadda haɗarin samar da kuɗaɗen ta’addanci ke gudana a cikin wannan ɓangare, tare da samar da hanyoyin da za su inganta sa ido da kulawa daga hukumomi.

Haka kuma, ya buƙaci haɗin kai, gaskiya da buɗaɗɗen aiki daga duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar wannan tsari.

Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki, Abubakar Bagudu, ya yaba wa wannan shiri, yana mai cewa haɗin gwiwar gwamnati da ƙungiyoyin farar hula na da matuƙar muhimmanci wajen yaƙi da laifukan tattalin arziki.

Shi ma Daraktan SCUML na EFCC, Harry Erin, ya ce wannan sabon bincike zai ba Nijeriya damar sake nazarin haɗarin da ke tattare da wannan ɓangare tun bayan binciken da aka yi a 2023.

Wannan gargaɗi ya zo ne a daidai lokacin da hare-haren ta’addanci ke sake ƙaruwa a ƙasar, musamman a Arewa maso Gabas, inda Boko Haram da kuma ISWAP ke ci gaba da addabar jama’a. A baya-bayan nan ma, wasu hare-haren bom sun yi ajalin mutane da dama a Maiduguri, lamarin da ya ƙara jaddada girman matsalar.

Masana tsaro sun nuna cewa ɗaya daga cikin manyan dalilan da ya sa wannan ta’addanci ke ci gaba shi ne hanyoyin samun kuɗi daga ciki da wajen ƙasa. Duk da cewa wasu ƙasashe sun ɗauki matakai na dakatar da tallafin da ake zargin yana kai wa ga ‘yan ta’adda, har yanzu ayyukansu na ci gaba da ƙaruwa da muni.

A wannan yanayi mai sarƙaƙiya, ƙaddamar da wannan tsarin NTFRA wani muhimmin mataki ne na daidaita tsarin yaƙi da ta’addanci, musamman wajen rufe hanyoyin samun kuɗaɗen da ke tallafa wa waɗannan ƙungiyoyi. Haka kuma, yana da matuƙar muhimmanci a tilasta wa ƙungiyoyin sa-kai bin ƙa’idojin gaskiya da riƙon amana, tare da tabbatar da cewa suna aiki ne cikin dokokin da aka kafa su.

A ƙarshe, dawo da amincewar jama’a ga waɗannan ƙungiyoyi da kuma tabbatar da tsaron ƙasa na buƙatar haɗin kai tsakanin gwamnati, hukumomi da kuma al’umma baki ɗaya. Yaƙi da ta’addanci ba na bindiga kaɗai ba ne, har ma na tattalin arziki da tsarin kula da kuɗaɗe.

By ukarofi