Gidauniyar Kannywood ta yi jimamin rasuwar Hajiya Sadiya da Umar Ascon

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gidauniyar Kannywood ta yi jimamin rashin wau fitattun jaruman finafinan Hausa, wato Hajiya Hajiya Sadiya da Umar Ascon.

Hajiya Sadiya, wadda aka fi sani da Sabuwa matar Ayuba Mai-Gadi ta cikin shirin Daɗin-Kowa a tashar Arewa24 da kuma Malam Umar Ascon da aka fi sani da Alhaji Lado na shirin Garwashi na UK Entertainment sun rasu ne a ‘yan kwanakin nan.

A sanarwar da gidauniyar ta fitar ta hannun Sakataren yaɗa labaranta, Yakubu Liman, ta bayyana cewa “jaruman biyu sun bayar da gagarumar gudunmawa a masana’antar Kannywood a irin rawar da suka taka a musamman a fitattun shirye-shiryen biyu.”

Ta ce, sun kasance masu jajircewa da aiki tuƙuru da halayye nagari a duk mu’amalarsu da ’yan uwa da kuma sauran abokan aiki.

A cewar gidauniyar, a tsawon lokacin da suka shafe na aiki, “Hajiya Sadiya da Malam Umar sun taka muhimmiyar rawa wajen ɗaga darajar shirya fina-finai a Kannywood musamman a shirye-shiryen da suke fitowa don amfanin jama’a da suka yi fice.”

Don haka ta bayyana rashin waɗannan abokan aiki biyu a matsayin babban rashi ga Kannywood da kuma masana’antar fina-finai ta Nijeriya baki ɗaya.

Hajiya Sadiya, ta rasu ne a daren Laraba bayan fama da rashin lafiya, kamar yadda rahotanni suka bayyana. An kuma a yi jana’izarta a yau Alhamis. Yayin da Alhaji Lado ya rasu a ‘yan kwanakin da suka gabata.

A ƙarshe gidauniyar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalai da ‘yan uwa da abokan aiki da kuma sauran masoya a
wannan lokaci mai cike da jimami tare da musu addu’ar gafarar Allah, musamman a wannan wata na azumi mai alfarama gami da bai wa iyalansu haƙurin rashin su.

By Babaji