Sheikh Lukuwa ya bijire wa umarnin Sultan, ya yi sallar idi yau a Sokoto

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Wani malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Musa Lukuwa, ya jagoranci mabiyansa wajen gudanar da sallar idi a ranar Alhamis, saɓanin umarnin da majalisar sarkin musulmai ta bayar. Wannan ya zo ne bayan Saad Abubakar ya ayyana Juma’a a matsayin ranar Sallah, sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Lukuwa ya jagoranci sallar ne a masallacinsa da ke Mabera da misalin ƙarfe 9:10 na safe, bayan ya yi bayani ga mabiyansa kan dalilan ɗaukar wannan mataki. Ya ce ya samu sahihan rahotanni na ganin jinjirin watan a Jamhuriyar Nijar, wanda ya ce ya dace a yi aiki da su bisa kusancin ƙasashen biyu.

Malamin ya bayyana cewa matakin da ya ɗauka ba rashin biyayya ba ne ga Sultan, sai dai bin koyarwar addini. Ya ce duk da cewa suna bin sanarwar Sultan wajen fara da kammala azumi, dole ne su yi aiki da sahihan shaidun ganin wata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, ko da kuwa hakan ya saɓa da sanarwar hukuma.

Haka kuma, ya tuna da yadda a baya malamai kamar Abubakar Mahmoud Gummi ke sanar da ganin wata daban, kafin a mayar da tsarin ƙarƙashin Sultan domin tabbatar da haɗin kai. Duk da haka, Lukuwa ya nace cewa a wannan karon sanarwar Sultan ba ta dace ba, don haka mabiyansa ba za su bi ba.

By ukarofi