Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
A wata takardar sanarwa ɗauke da sa hannun babban jami’in hulɗa da jama’a na gwamnan,Dikko Raɗɗa ya taya al’ummar jihar Katsina murna zagayowar ƙaramar sallah.
Gwamnan mai riƙe da sarautar Gwagwaren Katsina ya kuma taya al’ummar musulmi a jihar murnar kammala azumin watan Ramadan tare da kira da samun haɗin kai da kaunar juna a tsakanin al’ummar jihar.
“A lokacin gudanar da bukukuwan Sallah,ina kira da Musulmi da su ƙaunaci juna,su haɗa kansu da zama masu wadatar zucci kamar yadda muka nuna a cikin watan Ramadan,”inji malam Dikko.
Yayi fatan darussan da Musulmi suka koya a cikin watan Ramadan ya zama mai kariya a gare su na harkokin yau da kullum da zama nau’i zama tsintsiya maɗaurin ki ɗaya.
Gwamnan ya yi godiya ga Allah da ya ba ɗaukacin Musulmi damar kaiwa wannan wata mai tsarki,ya bayyana cewa darussan da watan Ramadan ke koyarwa na jin ƙai da sadaukar da kai ya kamata su wuce nan.
Malam Dikko Raɗɗa sai yayi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da gudanar da addu’a na samun zaman lafiya, tsaro da cigaban jihar.
Gwamnan yanzu haka na cikin tawagar shugaban ƙasa Bola Tinubu a wata ziyarar aiki a ƙasar Ingila.
