Yaƙin Gabas ta Tsakiya: Isra’ila ta sake halaka wani jagoran tsaron Iran

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Isra’ila ta sanar da halaka Ministan Leƙen Asirin Iran, Esmail Khatib a wani yanayi na ƙamarin rikici tsakanin ƙasashen a yankin Gabas ta Tsakiya.

Ministan Tsaron Isra’ila, Isreal Katz ya sanar da haka a wata sanarwa a ranar Laraba, inda ya ce hakan wani ɓangare ne na harin manyan jami’an gwamnatin Iran a yayin yaƙin.

Ya ce, an umarci rundunar sojin Isra’ila da su cigaba da kai farmaki akan dukkan manyan jami’an ƙasar waɗanda suke zama barazana a rikicin ɓangarorin.

Hakan na zuwa ne bayan rahoton halaka Ali Larijani, wanda shi ma babban jami’in gwamnatin Iran ne.

Zuwa yanzu dai ƙasar Iran ba ta tabbatar da kisan Khatib ba a hukumance, saidai ta yi alla-wadai da ire-iren hare-haren da cin alwashin ramako.

Tun a ƙarshen watan Fabarairu ne rikici tsakanin Isra’ila da Iran ya fara ƙazancewa bayan hare-haren haɗaka ta sama tsakanin Amurka da Isra’ila sun yi ajalin jagoran addinin Iran, Ali Khamenei, inda daga bisani rikicin ya faɗaɗa a shiyyar.

By Babaji