Shettima ya ziyarci waɗanda harin boma-boman Maiduguri ya shafa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, ya jaddada matakin Gwamnatin Tarayya na kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya, yana mai cewa waɗanda suke da hannu a hare-haren kwanan nan za su fuskanci hukuncin doka.

Shettima ya ce, baya ga umarnin shugaban ƙasa ga jagororin tsaro na su tare a Jihar Borno, Gwamnatin Tarayya tana ƙara ƙarfafa wa dakarun tsaro da kayan yaƙi domin yaƙar ta’addanci a sassan ƙasar da ke cigaba da addabar al’umma.

Shettima ya bayyana haka ne a jiya Laraba a Maiduguri yayin wata ziyarar duba marasa lafiyar da harin bom ya rutsa da su a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da ke Jihar Borno.

Mai taimaka masa akan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha ya bayyana haka a wata takarda, inda ya ce mataimakin shugaban ƙasar ya yi alla-wadai da hare-haren ƙunar baƙin-waken da suka shafi sama da mutane 100 waɗanda daga cikinsu sama da 20 suka rasu.

Ya bayyana waɗanda suke da hannu a ciki a matsayin marasa imani, yana mai cewa babu dalilin halaka waɗanda ba su ji ba, ba su gani ba.

A cewarsa, ziyarar tasa ta ƙunshi manufar jajenta wa waɗanda suka jikkata da iyalan mamatan, inda ya kuma tabbatar musu da samun tallafin gwamnati ta hannun Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA), Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas da kuma Gwamnatin Jihar Borno.

A yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙasar ya samu rakiyar Mataimakin Gwamnan Borno, Usman Kadafur; Darakta Janar ta NEMA, Zubaida Umar; Daraktan Lafiya na Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri, Farfesa Ahmed Ahijo, da wasu manyan jami’an gwamnati.

By Babaji