Gidauniyar Mangal ta kashe Naira milliyan 257 domin kula da marasa galihu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wani mai taimakon al’umma, Alhaji Dahiru Mangal, ya biya kuɗaɗen magani dana aiki da suka haura naira miliyan 257 ga kusan marasa lafiya 21,000 masu rauni a Jihar Katsina, daga 2016 zuwa yanzu.

Wani mamba na kwamitin amintattu na Gidauniyar Mangal, Alhaji Hassan Kabir, ne ya bayyana haka a ranar Asabar a Katsina, yayin tantance marasa lafiya masu matsalolin ido.

Kabir ya bayyana cewa a cikin wannan lokaci, gidauniyar ta ɗauki nauyin jinyar kusan marasa lafiya 3,000 masu cututtukxan fitsari (urology), da kuɗin da ya haura N140 miliyan.

Bugu da ƙari, Kabir ya ce fiye da marasa lafiya 17,000 da ke fama da matsalolin ido daban-daban sun samu kulawa, tare da kashe fiye da N30 miliyan.

Ya ƙara da cewa gidauniyar ta tallafa wa sama da marasa lafiya 1,000 masu fama da kumburin maraina (hernia) da hydrocele, inda ta ware aƙalla N87 miliyan domin kula da su.

Kabir ya bayyana cewa marasa lafiya da ƙananan cututtuka ana duba su, ana yi musu magani, ana ba su magunguna kyauta sannan a sallame su.

“Waɗanda ke buƙatar tiyata, gidauniyar ce ke ɗaukar nauyin dukkan kuɗaɗen aikin, har sai an sallame su daga asibiti.

“Gidauniyar ta gana da ƙwararrun likitoci kuma ta sayi kayan aikin likitanci da magunguna masu inganci domin waɗannan ayyuka,” in ji shi.

Ya bayyana cewa gidauniyar, wadda aka kafa a 2016, tana da burin tallafawa masu rauni ta hanyar kiwon lafiya, ilimi da kuma ƙarfafa tattalin arziki.

“Tun kafa ta, ta kuma ɗauki nauyin dubban ayyukan tiyata ga marasa lafiya daga jihohi makwabtaka har ma da Jamhuriyar Nijar.

“Manufarmu ita ce rage wa talakawa nauyin kuɗin jinya, musamman waɗanda ke da ƙalubalen biyan buƙatun yau da kullum,” in ji Kabir.

Wani Malamin jinya mai kula da cututtukan ido a Cibiyar Ido ta Katsina, Malam Ibrahim Lawal-Rabo, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa yana da matuƙar muhimmanci a wannan lokaci na ƙalubalen tattalin arzikin ƙasa.

Ya ce irin wannan aikin jinƙai na taimakawa wajen cike giɓin kula da lafiya, tare da ƙarfafa ayyukan gwamnati musamman a yankunan da ba su da wadatattun cibiyoyin lafiya.

Wasu daga cikin masu cin gajiyar sun yaba da tallafin gidauniyar tare da kira ga hukumomin gwamnati, ƙungiyoyi masu zaman kansu da masu hannu da shuni su yi koyi da kyakkyawar hanyar taimakon Mangal.

By ukarofi