Gobara ta kashe mutum biyu a Nijar

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga ƙasar Nijar mai maƙwabtaka da Nijeriya sun ce, mutum biyu sun mutu yayin da wasu sun jikkata sakamakon gobarar da ta tashi a kamfanin SONIDEP da ke birnin Zinder.

Rahotanni na nuni da cewa, iftila’in ya faru ne a ranar Labara a wani wurin ajiyar man fetur na kamfanin da lamarin ya shafa.

Haka nan, an ce gobarar ta ƙone wasu motocin dakon man fetur biyu ƙurmus.

A cewar majiyarmu, gobarar ta tashi ne a daidai lokacin da motocin dakon man suke ƙoƙarin sauke mai a ma’ajin man kamfanin na SONIDEP.

Ta ce gobarar ta haifar da ruɗani da fargaba a cikin zukatan mazauna yankin duk da cewa jami’an tsaro sun killace yankin domin bada kariya ga mutane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *