Alhazan Zamfara na hanyar komowa gida

Daga BASHIR ISAH

A wannan Alhamis alhazan Jihar Zamfara na hanyarsu ta komowa gida bayan kammala Hajjin 2023.

Bayanan Hukumar Aikin Hajji ta Nijeriya (NAHCON), sun nuna jirgin sama na kamfanin FLYNAS mai lamba XY7954 ya baro Jidda zuwa Sakkwato ɗauke da alhazan Jihar Zamfara 383 da kuma wasu jami’ai biyu.

NAHCON ta ce jirgin ya baro Jidda ne da misalin ƙarfe 12:23 na rana.

Da wannan, hukumar ta ce baki ɗaya adadin alhazan Nijeriya da aka yi nasarar dawo da su gida tun bayan kammala Hajjin na bana, ya kama mutum 3,427 a tsakanin sawun jirgi 9.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *