Buhari bai hana Shugaba Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba – Garba Shehu

Daga UMAR GARBA a Katsina

Kakakin tsohon shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya bayyana cewa tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, bai hana Shugaba Bola Ahmed Tinubu binciken jami’an gwamnatinsa ba.

Malam Garba Shehu ya bayyana haka ne cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Tiwita inda ya kuma musanta cewa tsohon Shugaban ƙasar yana katsalandan a binciken da sabuwar gwamnati ke son yi kan jami’an gwamnatin da ta gabata.

“Idan za a yarda da abin da aka ce a soshiyal midiya, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yana buƙatar mutumin da ya gaje shi, Shugaba Bola Ahmed Tinubu kada ya binciki tsoffin jami’an gwamnatinsa.

Wannan labarin ƙarya ne, kada ma mu tattauna a kansa ko mu mayar da hankali a kansa.

Wannan ƙarya ce tsagwaronta”, a cewar saƙon.

Wasu bayanai sun ce tsohon Shugaban Ƙasa Muhamadu Buhari ya gana da Shugaba Tinubu a birnin London domin rarrashinsa kada ya binciki tsoffin jami’an gwamnatin nasa.

Sai dai Malam Garba ya ƙaryata hakan, inda ya ƙara da cewa “babu kowa a ɗakin da suka gana sai su biyu kaɗai, don haka babu wanda ya isa ya bayar da labarin abin da suka tattauna a kai.”

A cewarsa, tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari yana yin bakin ƙoƙarinsa wajen ganin bai janye hankalin sabuwar gwamnati ba.

“Ya zaɓi ya tafi Daura domin fatan samun nutsuwa amma da ya fahimci hakan ba mai yiwuwa ba ne, masu ziyara na zuwa wajensa ba dare ba rana, shi ya sa ya tafi wani wuri da ke nesa,” inji sanarwar.

Tsohon shugaban yana fatan a bar shi ya huta kamar yadda ya kamata, kuma a bari gwamnatin Shugaba Tinubu ta samu zarafin gudanar da ayyukanta don cika alƙawuran da ta ɗauka.