Gwamna Abba da Honorabul Rabiu Gwarzo sun kawo cigaba a hukumar KSSSMB — Bashir Mu’azu

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano 

Daraktan Tsare-tsare, Bincike da ƙididdiga na Hukumar Kula da Manyan Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSSMB), Malam Bashir Mu’azu, ya bayyana cewa tun lokacin da ya shafe fiye da shekaru 30 yana aiki a ƙarƙashin hukumar, bai taɓa ganin shugaba mai nagarta da ƙwarewa kamar Hon. Rabiu Sale Gwarzo ba.

Ya ce hakan ne ma ya sa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Gwamnan Ilimi, ya zabi Rabiu Sale Gwarzo a matsayin Shugaban Hukumar KSSSMB, bisa la’akari da jajircewarsa, kyakkyawar mu’amala, da shugabanci na gaskiya.

Malam Bashir ya bayyana haka ne yayin bikin Ranar Malamai ta Duniya, inda ya wakilci shugaban hukumar a wajen taron. A cewarsa, wannan rana tana da muhimmanci matuƙa wajen tunatar da malamai da ɗalibai da sauran masu ruwa da tsaki game da rawar da suke takawa wajen inganta ilimi da tarbiyya.

Ya ce Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da jajircewa wajen haɓaka harkar ilimi, musamman ta hanyar ware kudade masu yawa a kasafin kuɗin 2024 da 2025, wanda hakan ya sa jihar ta zama kan gaba a sakamakon jarabawar NECO a Nijeriya.

A ƙarshe, Malam Bashir ya yaba wa ƙungiyar Malamai ta NUT reshen Kano a ƙarƙashin Kwamared Baffa Ibrahim Garko bisa gudanar da bikin ranar cikin nasara. Haka kuma, ya ambaci yadda Cibiyar Wayar da Kan Jama’a da Kyakkyawan Shugabanci (Center for Public Enlightenment and Good Leadership Deɓelopment – CEGLD) ta baiwa Hon. Rabiu Sale Gwarzo lambar yabo saboda nagartarsa, wanda Shugabar ANCOPSS, Hajiya Uwani Ahmad Balarabe, ta tabbatar da shi.

By ukarofi