Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya nemi ɗaukacin shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Kano da sauransu, da su yi koyi da shugaban hukumar Makaratun Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano wato, Kano State Science And Technical School Board STSB, Farfesa ɗahiru Sale Muhammad, kan gabatar da ayyuka 360 a shekara guda da naɗa shi shugaban hukumar ta STSB.
Wannan bayanin yabawa da neman a yi koyi da shugaban STSB, ya fito ne daga bakin wakilin gwamnan Kano, kuma kwamishinan ilimi na jihar, Hon. Umar Haruna Doguwa wanda ya wakilci Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf a wajen taron karramawa da yabawa da ma’aikatan hukumar makarantun kimiyya da fasaha ta jihar suka shiryawa Farfesa ɗahiru Sale Muhammad kan nasarar da ya samu na ayyuka 360 cikin shekara guda da ya yi a ofis, a taron da aka gabata a ƙarshan makon da ya gabata.
Haka shi ma, Hon. Haruna Umar Doguwa, ya ƙara da cewa irin ayyuka na cigaba da wannan hukuma ta samu ya ƙarfafa gwiwar gwamnatin Kano na fito da wasu tsare-tsare da ilimin kimiyya da fasaha wanda shi ne duniya ke yayi a yanzu, wanda ganin haka ne ya sa gwamnan Jihar Kano ke bai wa ilimi fifiko a kasafin kuɗi tun daga hawa gwamnan har zuwa yau inda a karon farko a bara 2023 aka ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kuɗi kan ilimi, bana 2024 kashi 31 aka ware a kasafin jihar Kano kan ilimi wanda ya nuna Jihar Kano ce ke ware kaso mafi tsoka a tarihin ƙasar nan.
A nasa jawabin, mai bawa gwamna Kano shawara kan al’amuran siyasa Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikata na ofishin mai baiwa gwamna shawara kan al’amuran siyasa, Dags Hon. Ayuba Doka Dawa, ya ce dama bai yi mamaki ba tun da wannan gwamnati manufar ta ilimi har zuwa ta biyu da ta uku, manufar gwamnatin Kwankwasiyya shi ne ilimi kuma wannan ce ta jawowa jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abba, ta samar musu da farin jini a siyasar Kano dama Arewa baki ɗaya, don haka wajibi ne a yaba wa Farfesa ɗahiru Sale, da kuma yin koyi da shi a dukkan wani muƙami da aka bai wa wani mutum a gwamnatin Abba Kanawa.
A ƙarshe Farfesa Dahiru Sale Yahaya godiya ya yi ga Ubangiji da kuma Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da ɗaukacin ma’,aikatan STSB, kan wannan yabo da karramawa da su ka yi masa, taron dai ya samu halattar malaman jami’a irin su Farfesa Abubakar S. Garba wanda ya wakilci mataimakin shugaban Jami’ar Northwest da sauran, jami’an gwamnati, ‘yan siyasa da sauransu, wanda suka haɗa da Hon. Abdulaziz Hasken Dala, Kansilan Ilimi na ƙaramar hukumar tsohon kantoman Dala, sai Hon. Gala kakakin ƙaramar hukumar Sumaila a Jihar Kano Nijeriya.
