Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa hedikwatar Kano da Jigawa ta Hukumar Kwastom ta Nijeriya kan rawar da ta taka wajen ƙara kuɗaɗen shiga da kashi 10.1 cikin ɗari daga watan Janairu zuwa Oktoban 2025.
A cewar bayanan da aka gabatar, sashen ya tara kuɗin shiga har Naira Biliyan 93.9 a cikin wa’adin, idan aka kwatanta da Naira Biliyan 85.3 da aka tara a shekarar 2024. Hakazalika, kuɗazen shiga daga Yankin Ciniki ‘Yantacce na Kano sun tashi daga Naira biliyan 2.6 a 2024 zuwa Naira biliyan 17.7 a 2025, abin da ke nuna ƙarin kusan kashi 582.93 cikin ɗari, sakamakon ingantaccen sa ido da kuma bin dokokin kasuwanci da ‘yan kasuwa suka ƙara yi.
Gwamna Yusuf ya bayyana wannan yabo ne ta bakin Kwamishinan Kasuwanci, Masana’antu da Zuba Jari na jihar, Shehu Wada-Sagagi, a wajen liyafar cin abinci da Dandalin Masu Ruwa da Tsaki na Kano/Jigawa ya shirya a Kano. Ya ce an shirya taron ne domin murnar fitowar sashen a matsayin hedikwatar da ta fi samun ci gaban kuɗaɗen shiga a taron shelf na Manyan Kwastom na shekarar 2025.
Gwamnan ya kuma yaba wa Babban Kwamandan Yankin, Dalhatu Abubakar-Zurmi, inda ya bayyana aikinsa a matsayin jajirtacce kuma abin koyi, wanda ya ginu kan ƙirƙire-ƙirƙire da bin doka da oda. Ya jaddada cewa nasarorin da sashen ya samu, musamman wajen kama muggan ƙwayoyi da suke barazana ga lafiyar al’umma, abin a yaba ne matuƙa.
Yusuf ya shawarci Dalhatu Abubakar-Zurmi da ya rubuta tarihin nasarorinsa domin zama darasi ga jami’an kwastom na gaba, yana mai cewa salon shugabancinsa ya kafa ma’aunin sabbin gyare-gyare da ayyukan kwastom na zamani. Ya taya sashen murna tare da yi masa fatan ci gaba da samun nasara wajen ƙarfafa kasuwanci da tsaron ƙasa.
A nasa jawabin, Dalhatu Abubakar-Zurmi ya gode wa Shugaban Hukumar Kwastom ta ƙasa, bisa amanar da aka ba shi ta jagorancin sashen Kano da Jigawa. Ya tuna cewa manufofin da ya kawo da farko ba su samu karɓuwa ba a ranar da ya karɓi aiki a 3 ga Fabrairun 2025, amma hacin gwiwar masu ruwa da tsaki ya sauya adawa zuwa cikakkiyar fahimta da amincewa.
Ya ce, an sauya yanayin aiki daga rikici zuwa jituwa ta hanyar wayar da kan jama’a, tsare-tsare na zamani da kuma sauƙaƙe hanyoyin aiki. Ya kuma bayyana cewa ‘yan kasuwa ne suka tallafa wa shirya liyafar ba tare da an ɗebo ko kwabo daga hukumar ba. Babban Kwamandan ya yaba wa jami’ansa, yana mai cewa suna da ƙwarewar jagorantar kowanne sashi a cikin hukumar.
Har ila yau, ya sake jaddada matsayar sashen ta rashin lamunta da safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba, yana bayyana cewa sabon tsarin zamani da ake bi yanzu ya zo ne domin ya zauna. Ya ce ko da ya bar aiki a yau, idan ya sake cin karo da ‘yan fasa-kwauri, ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen kama su.
Rahotan Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya ce sauran masu ruwa da tsaki a taron sun yaba da sauyin da aka samu a sashen, suna masu bayyana shi a matsayin wani ci gaba da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihinsa.
