Arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 3.98 a rubu’i na uku na 2025 – NBS

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar ƙididdiga ta Nijeriya, NBS ta ce arzikin da Nujeriya ke samarwa a cikin gida (GDP) ya ara da kashi 3.98 cikin 100 a rubu’i na uku na shekarar 2025.

Cikin rahoton da ta fitar, NBS arzikin cikin gida da Nijeriya ta samu a watannin rubu’i na uku na shekarar ya zarta wanda ta samu a daidai wannan lokacin na shekarar 2024.

NBS ta ce, fannin noma ne kan gaba a samar da arzikin da kashi 3.79 sai harkar masana’antu da ya aru da kashi 3.77.

A baya-bayan nan dai ana samun raguwar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, kamar yadda hukumar ta NBS ke fitarwa, wani abu da gwamnatin ƙasar ke dangantawa da matakan inganta tattalin arziki da take ɗauka.

By ukarofi