Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sabon rikici ya ɓarke a jam’iyyar APC bayan da tsohon ɗan majalisa, Sha’aban Sharaɗa, ya yi watsi da shawarar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, na mara wa ɗan majalisar wakilai, Sagir Koki, takara.
Sharaɗa, wanda ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai a shekarar 2019 zuwa 2023, ya shaida wa gidan rediyon Lumana Radio International a ranar Lahadi cewa, ba zai iya mara wa wani ɗan takara baya ba saboda daga mazaɓarsa ba matuƙar ba a bi tsarin da dimokraɗiyya ta tanada ba a lokacin da ake watsi da sauran ‘ya’yan jam’iyya.
Rahotanni sun nuna cewa Ganduje ya mara wa Koki baya wanda ke wakiltar ƙaramar hukumar birnin Kano a matsayin tikitin takara ta kai tsaye bayan sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC a watan da ya gabata.
“Muna maraba da dukkan waɗanda suka dawo jam’iyyar APC, amma abu ɗaya da ba za mu lamunta ba shi ne yi mana ƙarfa-ƙarfar ɗan takara. Wannan tsari ya gaza, kuma zai sake gazawa,” Sharada ya bayyana, yana buga misali da rikicin zaɓen da aka yi 2023 APC a Kano.
Ganduje an zarge shi ne da rashin tafi da jam’iyyar APC yadda ya kamata a Kano, wanda ya jawo rikicin da ya kai ga jam’iyyar ta gaza taɓuka komai a zaɓe a 2023.
Sharada na cikin ‘yan majalisar da ke tsagin tsohon gwamnan Kano, Ibrahim Shekarau wanda ke cikin G7, kuma sun zargi Ganduje a 2023 da mai da su saniyar ware a harkokin jam’iyyar da sauran matsaloli.
Sharada ya baya ya bar jam’iyyar APC zuwa jam’iyyar ADP tare da yin takarar gwamnan jihar Kano, sai dai bai yi nasara ba. Daga baya ya tsake dawowa jam’iyyar APC a shekarar 2023.
Matakin Ganduje na kwanan baya:
A makon da ya gabata, manyan ‘yan jam’iyyar APC a Kano, da suka haɗa da Sharada, sun ƙauracewa wani zama da tsohon shugaban jam’iyyar ta ƙasa, Ganduje, ya shirya wanda ke alamta yiwuwar samun rikicin cikin gida a jam’iyyar.
Ganduje ya shirya taron ne na tsawon kwana 4 domin tattaunawa a gidansa da ke Nasarawa GRA wanda ‘yan jam’iyyar masu goyon bayansa suka halarta daga ƙananan hukumomi 44.
Ya buƙaci ce da su nemi shugabanci gabanin gangamin taron da jam’iyyar za ta yi a watan Disambar APC.
Wasu majiyoyi cikin waɗanda suka halarci taron sun ce wannan dabara ce ganin ya cigaba da riƙe iko a jam’iyyar gabanin zaɓen cikin gida na jam’iyyar na shekarar 2027.
A yayin taron kamar yadda wani faifan bidiyo da ke yawo a shafin Facebook, ya nuna, sun nemi da a dawo da shugabancin jam’iyyar da ake da shi tun na shekarar 2023 da kuma ɗan takarar gwamna, Nasiru Gawuna.
ɗan takarar gwamnan jam’iyyar APC a zaɓen da ya gabata Gawuna da mataimakinsa Murtala Garo sun halarci taron tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar. Sai dai sanata Abdulrahman Sumaila da Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisa da kuma ‘yan majalisar wakilai Abdulmumin Jibrin da wanda ya dawo jam’iyyar APC a watannin baya ba su halarci taron ba.
Haka ma ministan gidaje da raya birane na ƙasa, Abdullahi Atah, tare da mataimaki ga shugaban ƙasa, Abdulaziz Abdulaziz da Bashir Lado, da sauran wasu ‘yan jam’iyyar APC ba su halarci taro ba.
Ganduje ya daga baya ya shaida wa manema labarai cewa taron an yi shi ne domin ƙarfafa haɗin kan ‘yan jam’iyyar da dawo da yarda da jaddada goyon bayan jam’iyyar ga shugaban ƙasa Bola Tinubu a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen tunkarar zaɓukan 2027.
“Mun yanke shawarar cewa mu tattara dukkan masu ruwa da tsaki da magoya baya domin bayyanawa a fili cewa muna goyon bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a matsayin ɗan takararmu tilp a zaɓen 2027,” inji Ganduje.
Ganduje ya kuma ba wa dukkan ofisoshin jam’iyyar APC a dukkan ƙananan hukumomi 44 da mazaɓu 484 umarnin buɗewa da motsa jam’iyya.
Ya kuma buƙaci a ƙara wayar da kan al’umma game da rajistar katin zaɓen da hukumar zaɓe ta INEC ke yi domin al’umma da ba su da ƙuri’a su yi rajista.
