Daga USMAN KAROFI
Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya kai ziyarar ta’aziyya ga Sarkin Zuru, Sanusi Muhammad Mika’ilu, bisa rasuwar Hajiya Hajara Hussaini, wadda aka fi sani da Innar Manir, mahaifiyar manajan daraktan kamfanin Zuru Building and Construction Company (ZBCC), Alhaji Adamu Hussaini. Gwamnan ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga iyali da kuma al’ummar Jihar Kebbi baki ɗaya.
A yayin ziyarar, Gwamna Aliyu ya yi addu’ar Allah Ya jikanta da rahama, ya sanya ta aljannatul firdausi, tare da bai wa iyalanta haƙurin jure wannan babban rashi. Ya tunatar da mahalarta cewa mutuwa hakki ce ga kowane rai, don haka wajibi ne a karɓi ƙaddarar Allah da zuciya ɗaya tare da ci gaba da yi wa mamaciyar addu’a.
Gwamnan ya kuma yaba da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin al’ummomin jihohin Sokoto da Kebbi, yana mai alƙawarin ci gaba da ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninsu. An gudanar da addu’o’i na musamman domin neman gafarar Allah ga marigayiyar da sauran musulman da suka riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Hajara Hussaini ta rasu ne a ranar Lahadin da ta gabata tana da shekaru 84 bayan doguwar jinya. Ta bar ‘ya’ya shida ciki har da Alhaji Adamu Hussaini da Dr. Manir Hussaini. Daga cikin waɗanda suka raka gwamnan zuwa ziyarar ta’aziyyar akwai Aliyu Magatakarda Wamakko, Bello Goronyo da sauran manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki daga Jihohin Sokoto da Kebbi.
