Daga USMAN KAROFI
Majalisar Dokokin ƙasar Ghana ta amince da wata doka mai cike da ce-ce-ku-ce wadda ke haramta ayyukan auren jinsi (LGBTQ+) tare da ƙara tsaurara hukunci kan masu alaƙa da irin waɗannan halaye. Dokar ta tanadi ɗaurin shekaru har uku a gidan yari ga mutanen da aka bayyana a matsayin masu alaƙa da LGBTQ+, sannan ta wajabta wa jama’a kai rahoton irin waɗannan ayyuka ga hukumomin tsaro.
A cewar masu goyon bayan dokar, matakin yana da nufin kare al’adu da kimar iyali ta al’ummar Ghana. Sun bayyana cewa dokar za ta ƙarfafa aiwatar da dokokin da ake da su tare da taimakawa hukumomi wajen daƙile abin da suka kira barazana ga al’adun ƙasar. Haka kuma ƙungiyoyin addini da dama sun nuna goyon bayansu ga dokar.
Sai dai dokar ba ta tsaya ga masu alaƙa da LGBTQ+ kawai ba, domin ta kuma shafi waɗanda ke bayyana goyon baya ko fafutukar kare haƙƙinsu. Irin waɗannan mutane na iya fuskantar hukuncin ɗauri idan dokar ta fara aiki. Duk da haka, an ce akwai keɓancewa ga lauyoyi, ‘yan jarida da ma’aikatan lafiya da ke gudanar da ayyukansu na ƙwararru.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun soki dokar, suna gargadin cewa za ta iya ƙara nuna wariya da tsangwama ga masu alaƙa da LGBTQ+ tare da ƙarfafa sa ido daga jama’a. Dokar yanzu tana jiran amincewar Shugaban Ghana, John Mahama, kafin ta zama doka. Idan aka sanya mata hannu, Ghana za ta shiga cikin jerin ƙasashen Afirka da suka ƙara tsaurara matakai kan LGBTQ+, ciki har da Uganda da Senegal.
