‘Yan bindiga sun sace Janar Rabe Abubakar da matarsa rana-tsaka a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

‘Yan bindiga sun sace tare da garkuwa da tsohon daraktan yaɗa labarai na rundunar sojojin Najeriya Manjo Janaral Rabe Abubakar da mai ɗakin sa a garin Matazu bisa kan hanyar na zuwa Katsina.

Sai dai direban sa ya tsira da rauni a jikin sa bayan harbin bindida daga maharan, kamar yadda Birgediya Janaral Sagir Musa mai Ritaya ya fitar da sanarwa cewa yanzu haka motar shi Janaral Rabe ƙirar Peugeot 504 mai kalan ja na nan ajiye a ofishin ‘yan sanda na garin Matazu.

Janaral Rabe Abubakar ɗan asalin ƙaramar hukumar Batsari na kan hanyar sa na zuwa gida Batsari kafin ya gamu da wannan bala’i.

Ya taba zama a Ƙofar Sauri da ke garin Katsina a lokacin da ya ke aikin soja yana da mukamin Manjo.

Ya zuwa yanzu babu wanda ya san inda ‘yan bindigan suka kai wannan tsohon babban soja da mai ɗakin sa,haka kuma babu wani bayani daga rundunar ‘yan sanda na Katsina.

By ukarofi

Leave a Reply