Daga USMAN KAROFI
Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama ministan tsaro na Najeriya, Christopher Gwabin Musa, da lambar yabo ta Grand Commander of Southern Kaduna (GCSK) bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya, tsaro da haɗin kan ƙasa.
An gudanar da bikin karramawar ne tare da halartar sarakunan gargajiya, shugabannin siyasa, wakilan al’umma, ƙungiyoyin matasa da na addinai, da sauran jama’ar Kudancin Kaduna. Yayin karɓar lambar yabon, Janar Musa ya gode wa al’ummar yankin bisa wannan girmamawa, yana mai bayyana Kudancin Kaduna a matsayin yanki mai albarka da ɗimbin damar ci gaba.
Ministan ya sadaukar da lambar yabon ga dukkan ‘yan Najeriya masu kishin ƙasa da zaman lafiya. Ya kuma buƙaci matasan yankin da su kasance masu bin doka da oda tare da kaucewa duk wani abu da ka iya haddasa rikici ko aikata laifuka. A cewarsa, tabbatar da tsaro nauyi ne na kowa da kowa, don haka ya zama wajibi ga masu ruwa da tsaki su haɗa kai wajen yaƙi da rashin tsaro.
Haka kuma, Janar Musa ya yabawa shugabannin al’umma bisa rawar da suke takawa wajen tattara bayanan sirri, yana mai kira gare su da su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai kan ayyukan masu aikata laifuka. Ya kuma buƙaci jama’ar yankin su ci gaba da rungumar ɗabi’un aiki tuƙuru, biyayya ga doka, sadaukarwa, hidima da tawali’u, yana mai jaddada cewa zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙin ci gaban ƙasa.
Da yake jawabi a wajen taron, shugaban majalisar shugabannin Kudancin Kaduna, Akau Moses, ya bayyana Janar Musa a matsayin jakadan yankin wanda ya kawo wa Kudancin Kaduna da Najeriya ɗaukaka ta hanyar aikinsa na soja. Ya ce ƙwarewa, jajircewa da kishin kasa da Ministan ya nuna sun sa ya samu karɓuwa a matakin ƙasa da ƙasa, kuma wannan lambar yabo wata hanya ce ta girmama gudunmawar da yake bayarwa ga tsaron ƙasa tare da zama abin koyi ga matasan Najeriya.
