Daga USMAN KAROFI
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya ta samu nasarar kare kambunta na Unity Cup bayan da ta lallasa Jamaica National Football Team da ci 3-0 a wasan ƙarshe da aka buga a filin wasa na The Valley Stadium.
Najeriya ta fara wasan cikin ƙarfi, inda ɗan wasan tsakiya Alhassan Yusuf ya zura ƙwallon farko tun a minti na uku da fara wasa. Ƙwallon ta bai wa Super Eagles damar mamaye wasan tun daga farkonsa tare da nuna ƙwarewa da tsari a ƙarƙashin jagorancin mai horarwa Eric Chelle.
A karo na biyu na wasan, kyaftin ɗin tawagar kuma ɗan gaba, Terem Moffi, ya ƙara ta biyu ta hanyar bugun kai mai kyau wanda ya sanya Jamaica cikin mawuyacin hali. Najeriya ta ci gaba da matsa lamba har zuwa ƙarshen wasan.
A mintunan ƙarin lokaci, Alhassan Yusuf ya sake zura ƙwallonsa ta biyu a wasan, wanda ya tabbatar da nasarar Super Eagles da ci 3-0. Wannan nasara ta bambanta da ta bara, lokacin da Najeriya ta doke Jamaica ne ta hanyar bugun fenariti bayan fafatawa mai tsanani, lamarin da ya nuna ci gaba da ƙarfafa matsayin Super Eagles a gasar Unity Cup.
