Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da buɗe makarantar marayu a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Malam Dikko Raɗɗa ya buɗe makarantar marayu da yara marasa galihu a jihar.

Cibiyar Magnet Academy AL- HUDA da ke ƙasar Amurka ta assasa ginin makarantar.

A jawabin sa gwamna Raɗɗa ya bayyana mahimmancin tallafawa marayu da yace lada ne ba iyaka .

Sai yayi kira ga al’ummar musulmi da su tashi tsaye wajan taimaka wa marayu ta inganta rayuwar su da sa su cikin farin ciki.

Malam Dikko Raɗɗa ya kuma nuna jin daɗin sa ga yadda yaga tsarin ginin da kayayyakin da makarantar ta tanada na fara gudanar da karatun.

Gwamnan yayi godiya ga Malam Zaharaddeen Ibrahim, shugaban alummar musulmi na ƙasar Amurka da ya zaɓi Jihar Katsina a matsayin inda aka gina wannan makaranta.

Ya kuma yi alƙawarin bada gudummawa a hukumance da kuma na ƙashin kansa domin ganin wannan makaranta ta ɗaukaka.

A nasa jawabin Sarkin Hausawa na ƙasar Ghana, Alhaji Kabiru kadiri wanda ke cikin tawagar hukumar makarantar ya sanar da cewa ƙasashen Amurka, Ingila, Austaraliya, Uganda, Nijar da Nijeriya sune suka ɗauki nauyin kafa makarantar.

Shima shugaban al’ummar musulmi na ƙasar Amurka Zaharaddeen Ibrahim ya sanar da cewa ginin makarantar za a yi shi kashi kashi ne.

Ya bayyana cewa za a fara da sashin yara ƙanana(nursery) sai yan firamare da na sakandare kuma makarantar zata rinka ɗaukan nauyin yaran da suka nuna hazaƙa zuwa makarantun ƙasan waje.

Babu shakka samar da wannan makaranta a Katsina cigaba ne wajen haɓaka ilimin marayu da marasa galihu da basu cika samun damar yin karatu ba.

By ukarofi