Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Yanzu haka gwamnan Jihar Katsina ya sauka a Beijing ƙasar Sin shi da tawagar sa a ƙoƙarin sa na nemo masu zuba jari a jihar.
Wannan shine kama aiki na farko da yayi bayan kammala hutun wata ɗaya da yayi a ƙasashen waje.
Ana sa ran wannan ziyara da ya kai za ta taimaka wajen samo masu zuba jari a jihar wajan fannin samar da cibiyar ƙera na’urorin bada hasken wutan lantarki mai amfani da hasken rana.
Gwamna da tawagar sa za su kai ziyara a kamfanin Sinotruck da zai ɗauki har tsawon kwana biyar kafin su kammala ziyarar.
A tawagar sa akwai kwamishinan noma Farfesa Ahmed Muhammad Bakori da kwamishinan ciniki da masana’antu da sakataren sa na musamman Abdullahi Turai
