Gwamna Dikko Raɗɗa ya naɗa sabbin kwamishinoni a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan jihar Katsina ya ƙara yin sabbin naɗe-naɗe a cikin gwamnatinsa da suka haɗa da ƙarin wasu kwamishinoni da masu taimaka masa.

A wata takardar sanarwa da ya fitar jami’in yaɗa labarai na gwamna Muhammad Kaula, waɗanda gwamnan ya amince da matsayin muƙamin kwamishina sun haɗa da shugaban jam’iyar APC na jihar Katsina mai barin gado Alhaji Sani Aliyu Daura da Ali Ahmad sai Alhaji Mannir Ayuba Sullubawa.

Haka kuma gwamnan ya naɗa Barista Suleiman Mohammed Namadi a matsayin manajan darakta na hukumar kula da zaizayar ƙasa.

Malam Dikko ya ƙara naɗa mataimaka na musamman guda biyar da suka haɗa da
Ibrahim Danjuma, Jamila
Salman da Hon Mudassir Mati a matsayin mayan mataimaka na musamman.

Sai kuma Musa Dan Kawu da Abdulfatah Kafur a matsayin mataimakin na musamman.

Gwamnan ya tura sunayen kwamishinonin ga majalisar dokoki domin tantancewa da amincewa.

Dikko Raɗɗa ya umarci waɗanda aka naɗa da su daidaita kansu da manufofin gwamnati na “Buliding your future” tare da aiki tuƙuru wajen alƙawarin da ya ɗauka wa al’ummar jihar Katsina.

Ya taya waɗanda aka naɗa murna tare da bayyana ƙwarin gwiwar sa kan cewa za su kawo cigaba a fannoni daban daban da aka ɗora masu alhaki.

Gwamnan ya buƙace su da su kawo ƙwarewar su, gaskiya da jajircewa a sabbin muƙamin su a yayin da jihar ke tafiya bisa turban cigaba.

By ukarofi