Gwamna Matawalle ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya don taimakawa a kan sha’anin tsaro da lafiya

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan jahar Zamfara, Hon Bello Muhammad Mutawalle, ya gana da Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J Mohammed a garin New York don tattaunawa a kan hanyoyin samar da agaji na gaggawa ga jahar Zamfara, mussaman a kan lamarin tsaro da bunƙasa sha’anin lafiya da ciniki a jaharsa.

Gwamnan jahar Zamfara wanda tun farko ya amsa gayyatar Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya don zuwa ƙasar Amurka ya tattauna da ita a lokacin taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana yanzu haka a garin New York, inda ya samu isa ofishinta tare da kwashe lokaci suna tattauna batutuwa da hanyoyin da za a bi ga samar da tallafi da agaji ga ‘yan gudun hijira waɗanda ayyukan ta’addanci suka yi wa Illa a jihar Zamfara.

Gwamnan ya samu tabbaci ga Mataimakiyar Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya a kan ganin an bayar da tallafi na kayan aiki na gaggawa don samun nasara a kan yaƙi da cutar cizon sauro ga mata masu juna biyu da yara ƙananan da cutar take yi wa saurin lahani.

Sauran su ne, samar da ingantattun bayanai daga ofishin Sakataren Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya da za su yi amfani ga bunƙasa hanyoyin kasuwanci da saka jari don ciyar da tattalin arziki jahar gaba.

Amina Mohammed ta bai wa Gwamnan tabbaci na za ta yi duk abin da ya dace don ganin an taimaka wa al’ummar jahar Zamfara, mussaman mata masu juna biyu da ƙananan yara saboda inganta rayuwarsu da samar musu da rayuwa mai amfani da ci gaba.

Daga nan, ta jinjina wa Gwamnan Bello Muhammad Mutawalle dangane da ƙoƙarinsa na yaƙi da ayyukan ta’addanci tare da samar da bayanai na gaskiya da ke amfani ga yaƙi da ta’addanci da kuma ɗaukar matakai a kan fitar da jahar daga halin da take ciki, abin da ya buɗe hanyar samar da taimako da agaji da zai taimaki miliyoyin al’ummar Zamfara.

Tun da farko, sai da Gwamna Mutawalle ya yi wa Mataimakiyar Sakataren Janar bayani dangane da irin yanayin da al’umma jahar suka samu kansu da na yankin Arewa maso-yamma da ke fuskantar ƙalubalen rashin tsaro, talauci da ayyukan ta’addanci.

Ya bayyana cewar, ya samu ƙwarin guiwa daga goyon baya da ya samu daga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da kuma addu’a da fatan alheri na al’ummar Zamfara a kan ganin ya ɗauki matakai don nemo mafita ga waɗanan matsalolin.

Ya nuna godiyarsa ga irin karamcin da Mataimakiyar Sakataren Janar ta yi musu dangane da kyautatawa da kuma samun wannan damar da ta ba shi tare da ƙwarin guiwa a kan zuwansa Amurka don ganin an nemo mafita da bayar da gudumuwa mai amfani da za ta ciyar da Zamfara gaba shekaru masu yawa a nan gaba.