Jan kunnen da NYSC ta yi wa masu digiri kan runguma sana’a

Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Hidimar Ƙasa ta Nijeriya (NYSC) a kwanakin baya ta shawarci matasa mambobinta masu aikin hikidmar ƙasa bayan kammala digirinsu na farko da su rungumi shirye-shiryen fara kasuwanci da sana’o’i daban-daban na gwamnati da masu zaman kansu, don bunƙasa fasaha da ninka hanyoyin samun kuɗin shiga a gare su tare da kauce wa tsintar kai a halin zaman kashe wando bayan kammala hidimar ƙasar.

Haƙiƙa wannan kira yana da matuƙar muhimmanci, idan aka yi la’akari da halin da tattalin arzikin Nijeriya ke ciki da kuma alƙiblar da ya ke tunkara.

A wani lokacin ana alaƙanta muhimmancin kasuwanci ko sanar’ar kai tamkar yadda ruwa ke da muhimmanci ga rayuwar ɗan adam. Tabbas hakan ta ke kuwa, domin rayuwa ba za ta taɓa tafiya daidai ba ga wanda ba shi da abun yi ba.

Hakan ya sanya shugabar gudanarwa ta NYSC a Jihar Anambra, Yetunde Baderinwa, ta bayar da shawarar a sansanin ’yan hidimar ƙasar na ‘Nnamdi Azikiwe Unity NYSC Permanent Orientation’ da ya ke a Umuawulu/Mbaukwu a Ƙaramar Hukumar Awka ta Kudu, yayin gasar SAED da kuma baje koli.

Duk da cewa, komai rabo ne kuma komai da lokacinsa, samun aikin albashi ya yi wa haƙar zinare fintinkau ta fuskar wahala da kuma tsanani a Nijeriya. Wannan dalili ya sanya Baderinwa ta ce, haɓaka fasaha yana taimaka wa mutane, don ƙirƙirar sabbin hanyoyin samun ayyuka da hanyoyin samun kuɗin shiga da kuma samar da kwanciyar hankali ta samun abun yi da kuma rashin fargaba ta rashin aiki.

Ta ƙara da cewa, gaskiyar rashin aikin yi a Nijeriya ya sanya ya dace mambobin bautar ƙasa da sauran mutane su sami dabarun da za su hana dogaro da ayyukan biyan albashi na yau da kullum don su sami ƙarfin kansu da wasu ta fuskar tattalin arziki.

Mutane da dama masu kasuwanci kai kan dogara da kawunansu wajen biyan buƙatu. Tabbas masu kasuwancin kai babu ruwansu da dogaro a kan wasu mutanen wajen neman samun biyan buƙatunsu na rayuwar yau da kullum. Kasuwancin kai ta horar da masu ita ga kawar da kai daga abun hannun mutane.

“Akwai shirye-shiryen kasuwanci daban-daban da kuma hanyoyin samar da kuɗaɗe da Gwamnatin Tarayya ta tanadar don ‘yan kasuwar bautar ƙasa su runguma. Suna da kyau sosai suna da kuna riba, duk da babu yawa. Yi ƙoaarin shiga cikin su. Kada ku jira har bayan shekarar hidimar ku,” inji ta.

wannan ba ƙaramin jan hankali ba ne ga matasa masu tasowa, waɗanda suka ɗauka cewa, samun takardar digiri tamkar wani garanti ne da ya ke nuni da cewa, aikin yi ko wadata sun samu a gare su. A zahirin gaskiya ko kusa na haka ba ne. a taƙaice ma dai yanzu a halin da duniya ke ciki, ba a Nijeriya kaɗai ba, samun aikin yin na albashin da mutum zai iya rufa wa kansa asiri, ya zama abu mai matuƙar wahala ko da kuwa a ƙasashen da suka ci gaba.

A yanzu a duniya an fi bayar da muhimmanci ga ƙirƙirar hanyoyin samar da kuɗin shiga ta hanyar sana’o’i ko kuma kasuwanci na ƙashin kai. Bambancin kawai shi ne, babban abin da ya fi bai wa matasan wasu ƙasashen nasara shi ne, jajircewa da rashin kasala wajen neman na kansu.

Idan matashi ya sanya kasala a zuciyarsa, ya zauna yana tunanin a ba shi aikin yi kaɗai na albashi, to babu makawa zamani zai yi wa irin wannan matashin mai takardar digiri a hannu nisa ba tare da ya ankara ba. Yi amfani da ilimin da ka koya a jami’a wajen bunƙasa sana’arka ko kasuwancinka, don kai ma ka ɗauki wani aiki, maimakon ka zauna ka na jiran albashin gwamnati ko kamfani! Tuni duniya ta yi nisa fa!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *