Babu wani fim da ba za a iya yi a Kannywood ba’, inji Aminu Saira

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

A lokacin da Darakta Aminu Saira ya ke gudanar da aikin fim din ‘Labarina’ a shekarun baya, mutane da dama suna xaukar vata lokacin sa kawai ya ke yi saboda yadda a ke ganin fim mai dogon zango abu ne da ba ya cikin tsarin masana’antar finafinai ta Kannywood, shi kuma ya zo ya ke yi don haka wasu ke yi masa dariya saboda ya na zuba kuxin sa ne a wajen da ba zai dawo ba. To sai bayan tsawon lokaci da shigar masana’antar wani yanayi ne a ke ganin hanyar da Daraktan ya bi ita ce kawai za ta kawo mafita, wannan ta sa a ke kallon Darakta Aminu Saira a matsayin wani jagoran kawo sauyi a masana’antar. Wakilin mu a Kano Mukhtar Yakubu ya tattauna da Darakta Aminu Saira, domin irin hangen da ya yi wa harkar fim tun a wancan lokacin wanda hakan ya sa ya shirya fim din ‘Labarina’ mai dogon Zango, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda ta kasance.

Darakta Aminu Saira, kai ne mai bada Umarni a fim din ‘Labarina’, wanda a wancan lokacin da ka ke gabatar da aikin ana ganin kamar vata lokaci kawai ka ke ji, ko kuma kana zuba kuɗin ka a wajen da ba zai dawo ba, ko wane irin hange ka yi tun a baya ka samar da wannan fim ɗin na ‘Labarina’?
To da farko dai ni abin da na ke so a sanar da mutane shi ne; duk abin da za ka yi a rayuwa idan ka yi bincike iya wanda za ka yi kuma ka yunƙoro, kuma sai ka bar wa Allah ragowar. Da farko na yi bincike na yi nazari harkar fim mai dogon zango a duniya ta yi tasiri a duniya ba ma a nan ba, kuma tasirin sa ne ya sa har ya zo ya fara mamaye ƙasashen mu na Afirka to wannan ne ya sa na yi nazari na ga cewar za a kai lokacin da tasirin zai kai ga ko da ba mu yi da yaren mu ba, to na yaren wasu zai zo ya mamaye masar mu, wanda kuma an fara yin hakan, to sai na yi tunanin gara na shiga fagen, yadda za mu dakatar da yin fim masu gajeren Zango. Uma da yawa na samu surutu, mutane da yawa suna ganin vata lokaci ne, wasu na kallon ba ka san me ka ki yi ba ga wajen da ka ke da nasara ka ajiye ka tafi wani waje, to duk abin da na gama nazari na dai na riga na yi tunanin cewa bari na yi kuma na tsaya na gogara ga Allah, kuma cikin ikon Allah sai aka ga a yanzu an zo lokacin da aka saki fim cin ya zo daidai lokacin da fim mai dogon zango ya ke da tasiri ya mamaye Nigeriya da ma Afirka.

Kafin a fara harka ‘Labarina’, ana ganin ‘yan masana’antar Kannywood an yi musu nisan da ba za su iya kaiwa ga wajen ba, amma da aka fara haska ‘Labarina’, sai aka ga lallai akwai Kwarewar ba ta fito ba ne.
Yauwa ni abin da na ke gani shi ne, duk wani fim da a ke yin sa a duniya Kannywood za su iya yin sa, in da za a bada lokaci da kuma kasafin kuɗin da za a yi fim ɗin, sannan a zauna a yi bincike sosai, sannan a tsaya a jajirce a yi shi, don haka ni ban tava ji a raina ba cewar akwai wani fim da zai gagari masana’antar Kannywood, in ka ga ya gagari masana’antar to abu biyu ne, na farko, babu kuɗin da za a yi shi. Na biyu kuma in da kuɗin ba a tsaya an jajirce ba wajen aikin don haka duk wani abu da ƙwaƙwalwar wani Mutum za ta yi shi a duniya ni ina ganin in dai an tsaya, to za a yi shi a masana’antar Kannywood in dai an tsaya kuma an bada lokacin yin aikin, shi ya sa duk wani surutu da za a yi ba na kallon sa, kawai na yarda an yi mana nisa ta hanyar kafital, kuma lokaci ya na zuwa duk sanda Allah ya kaimu lokacin da muka mallaki wannan kuɗin to kuwa za a sha mamaki.

Tashin masana’antar da kuma shi kan sa fim ɗin ‘Labarina, wani abu ne da a ke ganin don an haska shi ne a tashar talbijin ta Arewa 24, ba don haka ba da ba zai yi tasiri ba.
Wannan wata magana ce ba za a ɗauke ta ba, domin idan ka duba fim nawa ne aka haska a Arewa wanda wasu na nan kuma ba su yi tasiri ba. Ba haka ba ne duk abin da ka ga ya yi tasiri ya ɗaukaka, akwai abu biyu. Na farko Allah shi ya ke ɗaukaka wa, ko an kai shi Arewa ko ba a kai shi ba idan Allah ya so zai ɗaukaka, ana gani fim nawa ne ba a kai su Arewa ba su ka ɗaukaka wanda a masana’antar Kannywood ɗin su ke wanda a ‘YouTube’ ma a ke ɗora su. Ai akwai finafinai irin su ‘Izzar so’, ‘A duniya’ da sauran su, fim ne da sun yi tasiri a cikin jama’a ba tare da ana haska su a wata tasha ba a kan ‘You Tube’ kawai a ke ɗora su. Kawai a daina wani tunanin sai an haska a wani wajen kawai fim idan Allah ya nufa zai yi nasara zai yi. Sannan kuma idan fim ya na da kyau, to shi ma wannan ko’ina ka kai shi a kwana a tashi sai ya bayyana kan sa don haka ni abin da na ɗauka kenan.

Bayan an kammala haska Zango na uku sai aka fara baza labarin ba za a ci gaba da kallon ci gaban shirin ba a Arewa 24, amma dai da aka dawo aka ci gaba da haskawa sai aka ga saɓanin yadda a ke haskawa a baya, domin a yanzu ba a yin maimaici kamar yadda a ke yi a baya.
E to, a wancan na farko Arewa 24 mun sayar musu da haƙƙin mallaka ne wato zango na farko da na biyu, don haka su ne su ke da iko da shi. To wannan lokacin kuma mun ƙara faɗaɗa kasuwancin mu ne, sai ya zamana lokaci muka saya wanda a yanzu mu ne mu ke da damar mu faɗi adadin da mu ke so a haska mana don haka mun sayi lokaci ne na Sa’a duga, muka bada dama tun da akwai wani gidan TV ɗin ma daban na wani tambari TV shi ma mun ba su damar su haska kuma akwai ‘YouTube Channel’ ɗin mu da mu ke haskawa, don dai a samu a ƙara hanyar samun kuɗin shiga, tun da fim ne da gaskiya ana kashe kuɗi a kan sa don haka ba zai yiwu mu takure tunanin mu a waje ɗaya ba, dole mu ƙara samar da hanyoyin da za mu rinƙa samun kuɗin shiga saboda abin da a ke kashewa lallai a tabbatar ya dawo har ma a samu riba, domin a samu ɗorewar yin sa ɗin kada a kasa, don haka tsarin da muka yi, muna ci gaba da yin fim ɗin, kuma muna ƙara faɗaɗa hanyoyin samun kuɗin shiga saboda a kwana a tashi yadda fim ɗin ya ke tafiya to kuma tsadar aikin ta na ƙaruwa ne, kowa ya san yadda rayuwar take kullum abubuwa ƙara tsada su ke yi. To idan muka ce za mu takura tunanin mu a waje ɗaya, za a kai lokacin da ba za mu iya ɗaukar nauyin fim ɗin ba, to don haka mu ke ta shigo da kamfanoni da sauran ma’aikatu domin ƙarin samun kuɗin shiga don kar abin a ce ya yanke ba a samu yin sa ba, to wannan gaskiya shi ne dalilin, kuma cikin ikon Allah sai muka samu nasarar yin hakan.

Bayan tunanin ka na samar da fim da zai kawo sauyi a masana’antar Kannywood, wanda a yanzu ka yi nasara. Wane buri kuma ka sa a gaba dangane da masana’antar na gaba?
E gaskiya ina da burin ba ma wai Kannywood ba, ba ma wai Nijeriya ba, ni yanzu burina shi ne ya za mu yi mu yi fim wanda zai yi tasiri ba ma wai a Nahiyar mu ta Afirka ba, ya zama fim ne wanda ya ke da tasiri a duniya, wannan shi ne babban burina, kuma in dai da rai da Lafiya wata rana in Allah ya yarda za mu cimma burin.

Kenan dai akwai wani yunƙuri da ka ke na samar da fim na gana.
E akwai domin ina ta shirya wani Labari, to amma dai a yanzu muna kan ‘Labarina’ daga yanzu har ƙarshan shekarar nan da ma sabuwar shekarar da za mu shiga muna nan a kan shi ‘Labarina’ ɗin. To amma dai muna ta yunƙurin samar da wani wanda a ƙalla zai fi ‘Labarina’, ko kuma su yi gogayya da shi, to amma shi ma dole ne abu ne da sai ka zauna ka yi nazari sosai, kuma in Allah ya yarda za mu kai ga nasara.

To daga ƙarshe wane kira za ka yi ga Jama’a musamman abokan mu’amalar ku?
To ni kiran da zan yi da su kamar kamfanonin suna buƙatar a tallata musu kayan su duniya ta gani, mu kuma muna da abin da jama’a su ke kallo, don haka muna kira da kamfanoni waɗanda za su iya zuwa su kawo hajar su, sai su zo mu yi haɗin gwiwa mu zauna mu yi abin da ya dace wajen tallata kayan su kuma masu kallon mu a yanzu ci gaba ya sa mun faɗaɗa wajen da mu ke saka fim ɗin mu don haka ba sai a Arewa 24 kaɗai za su kalla ba, don haka wanda bai samu dama ya kalla a Arewa ba, zai iya tafiya ‘You Tube’ ɗin mu, wanda duk ranar da za a haska a Arewa kusan tare ma mu ke sakawa, ko in ce ma minti talatin kafin a fara haskawa, to wannan shi ya fi sauƙi, domin idan ma ka wuce lokacin shi ya na nan a wajen za ka zo ka ci gaba da kallon sa don ba wai cire shi a ke yi ba , ina fatan Allah ya yi mana jagora a kan abin da muka sa a gaba.

To madalla mun gode.
Ni ma nagode sosai.