Mahdi Shehu ya nemi afuwar Gwamna Masari kan yaɗa bayanan bogi

Daga BASHIR ISAH

Shugaban kamfanin Dialogue Group, Muhammad Mahdi Shehu, ya miƙa ƙoƙon neman afuwa ga Gwamnan Katsina, Bello Masari kan cewa ya dubi Allah sannan ya yi masa afuwa dangane da bayanan ƙarya da ya ce ya yi ta yaɗawa a kan gwamnan da gwamnatinsa wanda suka taɓa mutunci da martabar gwamnan da ma gwamnatinsa.

Shehu ya nemi afuwar Masari ne cikin wata wasiƙa da ya fitar mai ɗauke da kwanan wata, 23 ga Satumban 2021.

Afuwar da Shehu ya nema ta haɗa har da ta al’ummar Jihar Katsina baki ɗaya bisa yadda ya yi ta yaɗa bayanan bogin da suka shafi gwamnatin jihar.

Shehu ya ce yana fata Gwamna Masari zai yafe masa dangane da dukkan bayanan ƙanzon kuregen da ya yi ta yaɗawa wanda ya taba mutuncin ba gwamnatin jihar kaɗai ba, har ma da jam’iyyar APC da kuma al’ummar jihar baki ɗaya.

Kazalika, baya ga yafiyar da ya nema Shehu ya kuma buƙaci Gwamna Masari ya yarje masa kan ya kai masa ziyara don ya gabatar masa da wasiƙar neman afuwar da kansa.

A can baya Muhammad Mahdi Shehu ya zargi Gwamnatin Jihar Katsina da wawushe kuɗin jihar har biliyan N52.6 daga asusunta a tsakanin shekaru biyar da suka gabata da dai sauransu.