Tashin gwauron zabin Dala

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ko yaya gauro a zabi ke tashi sama?, masu zabi za su iya ba mu amsa, amma a nan zan ce akan yi amfani da furucin in ana son kwatanta yadda wata haja kan zama in ta yi ɗan karen tsada. Za a fi gane batun in kai tsaye kawai a ka ce kaya sun yi matuƙar tsada. Ita dai dala takardar kuɗin Amurka ce da kuma a ke amfani da ita wajen harkokin cinikayya a duniya.

A ɗan tsakanin nan a Nijeriya dala ta yi matuqar tsada in an kwatanta ta da naira ta Nijeriya. Ni dai a iya sani na ba a taɓa samun lokacin da dala ta yi wannan tashin farashi ba. Tarihi ya nuna a zamanin mulkin marigayi Shehu Shagari wato jamhuriya ta biyu daga 1979 zuwa 1983 dala na kunnen doki da naira ne. In haka ya a ka yi yanzu sai an lale ɗaruruwan nairori kafin samun dala ɗaya?.

Wani ma abun tambayar shi ne mai ya haɗa tashin farashin dala da masu sayar da tattasai da tumatur, albasa, citta da sauran kayan da ‘yan Nijeriya ke samarwa? Masana tattalin arziki kan bayyana cewa buƙatun sayo kaya daga ƙetare da ƙasa ƙera ko samar da abubuwan da mutane ke buƙata daga cikin gida na daga dalilan da kan kawo tashin farashin dala. In kuwa haka ne ya nuna in an tada farashin kayan da a kan samar a gida to akwai zalama da rashin son sauƙi ga jama’a musamman talakawa.

Hakanan zai yi wuya gwamnati ta iya sa baki don a kan ga tamkar ta gaza daidaita farashin naira don haka wasu ‘yan kasuwa kan sanya farashin da su ka ga za su ci ƙazamar riba. Duk ƙasar da ta ari ɗabi’ar jari hujja a harkar saye da sayarwa, to sauqi na da wuyar samuwa. Yayin da sashin jama’a ke mallakar komai da su ke buƙata har ma waɗanda ba sa buƙata zuwa ƙarshen rayuwar su.

Yayin da wani kan samu kumburin ciki don tsananin koshi yayin da wani ke kwana cikin sa na kiran ciroma, ai an shiga zamanin “ka ci na ka in ci na wa ba rowa ba ne.” watannin baya na kan ce in ka je gidan mutum ka ga buhun shinkafa a jingine to wannan gidan na da wadatar abinci amma yanzu na sauya matsaya zuwa in ka je gidan mutum ka samu ya na da ɗan tumbin buhu na shinkafa kimanin kwano biyar to akwai wadatar abinci da ya dace har makwabta su shaida.

Labarun da a ke samu daga kasuwanni, na nuna ninkawar farashin muhimman kayan masarufi ciki kuwa da nama, dankali, doya, yakuza da alaiyafo da sauran su. Duk hujjojin kuma ba sa wuce tashin farashin dalar Amurka. Gaskiya abun da a shekaru goma zuwa sha biyar mutum kan cimma da naira dubu biyar yanzu sai naira dubu hamsin. Haka nan duk masu yin wata hidima ta naira dubu ƙari a baya yanzu za ka ji su na lissafin naira miliyan ne.

Mu na ‘yan yara na taɓa zuwa ɗaurin auren wani mai kuɗi a anguwar mu nan Jekadafari a Gombe a ka ce an ba da sadaki naira dubu!, sai da tamkar mu ka sararin da a ke ɗaura auren ya girgiza don jin nauyin kuɗin. Yau fa in an je ɗauren aure ai daga naira dubu hamsin ne zuwa sama inda naira dubu ɗaya ta zama kuɗin miƙa wa maroƙa masu ƙarajin an ba da kuɗi lakadan ba ajalan ba. Yaushe Nijeriya za ta aminta daga tsadar kaya a sanadiyyar tashin farashin dala?.

Dalar Amurka na cigaba da tashin gauron zabi a Nijeriya duk da barazanar cafke shugaban dandalin bayanan farashin canji na ABOKI FX da gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele ya yi.

In za a tuna Emefiele ya zargi mai dandalin ɗan Nijeriya mazaunin Burtaniya Olumide Oniwinde da tada farashin dala da sauran kuɗin ƙetare ta hanyar ba da farashin da ya wuce qa’ida a shafin na sa da mutane kan dogara da shi don sanin yadda canji ya kwana.

A daidai lokacin da Emefiele ya yi barazanar da ta sanya shafin ABOKI FX rufe sashin bayanan canjin naira ya koma na kuɗin yanar gizo wato CRYPTOCURRENCY an qara samun tashin farashin dalar da wajen Naira 5. Yanzu haka ai farashin na ƙara gaba ne a kusan duk bayan kwana biyu ko sati. Godwin Emefiele da tuni ya dakatar da ba da dala ga kasuwac canji, na ƙarfafa lalle mai son dala ya tunkari bankin sa da sahihan takardun tafiya, na magani ko kasuwanci don samun kuɗin bisa canjin gwamnati.

Hakanan in ma buƙatar mutum ta wuce mizani za a iya sanar da babban bankin don dubawa a biya buƙatar mai buƙata. Abun binciken shi ne a kan samu dalar ta wannan hanya cikin sauƙi kuma haƙiƙa waɗanda su ka cancanta ne a ke ba wa ko sai masu uwa a murhu? Na shiga kasuwar canjin a Abuja na samu ‘yan canjin na cigaba da harkokin su cikin natsuwa da fatar gwamnati ta sauya tsari don ci gaba da saƙo dalar maimakon dogaro ga masu fito da ita daga ma’ajiyar banki ko gida su na sayarwa don samun na kashewa.

A sharhin da ya saba yi a kafafen labaru ɗan canji Jibrin Zakar ya ce ba mai son tsadar kuma su ma ‘yan canji na iya asara ko riba ga yanda dalar ba ta da tabbas. Zakar ya ce ‘yan kasuwar a kullum na kwana da shirin asara ko riba domin duk hannun da ya kirga riba wataran zai ƙirga faɗuwa. Ɗan canjin ya buqaci gwamnan babban bankin na yanzu Godwin Emefiele ya kofi hanyoyin da tsohon gwamnan babban bankin kuma tsohon Sarkin Kano Sunusi Lamido Sunusi ya bi kan lamarin dala.

Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Nijeriya CBN Kingsley Moghalu ya shawarci gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya bar Naira ta sama wa kanta daraja a kasuwa. Moghalu ya wallafa a shafinsa cewa barin Naira ta nema wa kanta daraja shi ne hanya fitacciya ta farfaɗo da darajar Naira kan Dalar Amurka. Ya ƙara da cewa matuƙar ba a faɗaɗa tattalin arzikin Nijeriya waje da dogaro ga man fetur ba za a cigaba da samun ƙalubale.

Duk da haka wasu sun zargi Moghalu da cewa ya taimaka wajen faɗuwar darajar Naira lokacin ya na aiki a babban bankin don haka yanzu ba shi da hurumin ba da wata mafita.

Masanin tattalin arziki a Abuja Yusha’u Aliyu ya ce, matakan na gwamnati kan kasuwar canji ba za su zama da illar gaske ba inda a gefe a na lura da gaskiyar waɗanda kan samu dalar daga bankuna. Aliyu ya ce za a iya samun mai fama da ciwon kai zai karɓi dala a matsayin wanda zai tafi jinya ƙetare ko kuma a yi amfani da sunan kudin biyan karatun ɗalibai, alhali karkatar da kuɗin za a iya yi zuwa neman ƙazamar riba a cikin gida.

Ba a taɓa samun tashin dala a tarihi da ya kai wannan karo ba don ko lokacin da lamarin ya yi muni a wajajen 2015 farkon hawa mulkin shugaba Buhari, ta cilla zuwa N520 amma zuba dala a kasuwar canji ta sauko da ita zuwa ƙasa da Naira 400.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *