Kullen mace: Tsananin so, kishi ko rashin yarda?

Daga AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haɗuwa a filin Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Manhaja. A wannan mako kuma, mun kawo muku bayani a kan yadda wasu mazan aure musamman ma mazajen Hausawa waɗanda suke yi wa iyalansu kulle.

Mene ne kulle?

Kulle shi ne a hana mace ta fita ko ta yi mu’amala da waɗanda take so. Yawancin mazan Hausawa suna da kulle amma sai dai yayin da wasu mazan suke da sauƙi wajen mu’amala da tafiyar da iyali, wasu mazan kuma suna da zafin kishi da tsaurarawa. A yau za mu yi magana a kan masu tsaurarawar ne.

Kodayake, Musulunci ya koyar da mu yadda za mu yi zaman aure. Sannan ya zana wa kowa haƙƙoƙinsa a cikin zamantakewar aure. Inda aka nuna cewa, namiji shi ne shugaba kuma mai tsayawa ne a kan mata. Amma kuma ko ya halatta yadda wasu mazan suke tsaurarawa a wajen kulle?

Bayan an yi aure miji yana gani matar nan ta zama mallakinsa. Don haka, zai yi duk wasu abubuwa da zai wa kansa garkuwa don ta ci gaba da zama mallakinsa shi kaɗai. Kuma ta dinga masa biyayya tana jin maganarsa shi ɗaya. Sai ya fara bin wasu hanyoyi da za su taimaka masa.

Hanyoyin da wasu mazan suke bi don yi wa mata kulle:

Na farko, maza suna hana matarsu fita ko da zuwa nan da can. Sai gidan wanda suka yi niyya. Wani gidan iyayenta ma sai ta yi shekara da shekaru ba ta leƙa ba. Saboda yana gudun kada ta dinga haɗuwa da wasu mutanen ko da kuwa ‘yan’uwanta ne, domin kada su hure mata kunne a kansa. Saboda yana ganin rashin wayonta ko ƙarancin shekarunta. Sannan wani kuma yana tunanin idan tana haɗuwa da wasu ko da ‘yan’uwanta ne da mazajensu suka fi shi samu za ta raina ƙoƙarinsa. Wani kuma matarsa ce kawai ba ya son kowa ya gani. Wani idan ba danginsa ne suke sabga ba, ba zai bar ta ta je ba. Ko sabga ake a danginta ita kuma, ba ta da tabbas ko zai bar ta ta je. Wani ko asibiti da ya zama lalura ba ya son matarsa ta je.

Irin waɗannan mazaje sukan yi ƙoƙarin raba mace da kowa. Ta yadda za ta ƙara dogara da shi, ta dinga tsoron rabuwa da shi saboda ta rabu da kowa sanadiyyarsa. Ta zam ba ta da kowa, sai shi.

Na biyu, wasu mazan sukan hana kowa ya kawo wa matarsu ziyara sai wanda suka ga dama, suka yi niyya. Wani ko da ƙannenta maza ma sai ya hana su zuwa gidanta saboda wai kada su kalle masa matarsa.

Abu na uku da namiji mai kulle yake yi shi ne, ƙwace wayarta don kada ta yi mu’amala da kowa. Wani mai sauƙi- sauƙi ne ma zai ƙwace layukan da mutane suka santa da shi ya ba ta sabon layi. Saboda ya yanke mata mu’amala da mutanenta na da kafin ta shigo gidansa.

Wani kuma sai ya ƙwace babbar wayarta ya bar mata ƙarama wacce ba za ta iya hawa yanar gizo da ita ba. Saboda yana tsoro kada tarbiyyarta ta gurɓace. Wani kuma zai bar ta da wayar amma kullum cikin sa ido yake da bincike a wayar saboda kada ta yi mu’amala da waɗanda ba ya buƙata.

Na huɗu kuma shi ne, maza masu kulle sukan hana mata sana’a ko aiki ko ci gaba da karatu. Yana ganin ƙarin karatun zai sa idonta ya ƙara buɗewa ta raina shi. Wani kuma yana ganin yin sana’a da aiki zai sa ta tara dukiya ta kasa yi masa biyayya saboda ba abinda take nema a wajensa. Idan kuwa ya hana ta neman na kanta, ai dole ta zo masa da ‘yar murya ya ba ta wani abu. Shi kuma sannan zai nuna mulki.

Na biyar kuma, hana ta yin shigar da ranta yake so ko da a cikin gida ne. Akwai mazan da sam mace ko biki za ta je ba za ta yi shigar da take so ba ta yi ado. Sai ya umarce ta ta sa doguwar riga da zumbulelen hijabi a kai. Kuma duk zafi haka za ta fita. Wani ko cikin gidanta ba ta isa ta yi shiga irin wacce mata suke yi don faranta wa miji rai ba. Hasali shi shigar ma takaici take sanya masa. Ko yaransa waɗanda ba nata ba ne idan maza ne ba ya so su kalle ta. Sai kishi ya kama shi. Wani ma fa yaran ƙanana ne, ba su san wata sha’awa ba. Amma kishi yake da su.

Na biyar kuma shi ne, sanya mata tsoro a zuciyarta da danƙwafar da ita. Maza irin waɗannan suna danƙwafar da mace ta ma manta wacece ita. Sukan daka wa mace tsawa yadda suke yi wa ‘ya’yansu, wasu ma har da duka. Ko su ƙi kula ta ko hira da ita sai lokacin da suke buƙatarta. Duk wai don a sanya mata tsoro a ranta ta ji ita ba komai ba ce ta ci gaba da yi musu biyayya ko da a kan saɓon Allah ne. Wani har horon yunwa yake mata. Wani kuma har kulle mace yake a gida ya fita da mukullin idan ta ƙi yi masa biyayya.

Sannan na bakwai akwai wani mijin ma saboda tsananinsa dai-dai da abinci sai ya auna mata ya ba ta. Saboda kada ta yi masa almubazzaranci ko ta yi kyauta.

Amma kuma Yayana ka sani, shi yi wa mace kulle tamkar girman kai ba koyarwar addini ba. Kuma tauye haƙkin ɗan’adam ne. Duk da dai namiji yana ganin mace tana ƙarƙashin kulawarsa ne. Kuma a cikin yi mata tarbiyya ne hana ta cakuɗa da mutane da za su iya canza mata tunani shi ma duk ba laifi ba ne. Amma kada a wuce iyaka.

Sannan rashin yarda ba ƙaramar illa yake kawowa ba a kowacce alaƙa. Mu koma batun waya. Wata matar ba don komai take amfani da waya ba sai don yanar gizo. Kuma yanar gizo nan don sana’a take amfsni da shi. Ta nan take kasuwancinta. Ka toshe mata wannan hanyar ka ƙwace mata waya, kuma kana tsammanin ta so ka ko ta yi maka biyayya tsakani da Allah? Wata fa daga nan ka koya mata munafurci. Kuma da ma takurawa tana kawo haka. Za ta yi ta ɓoye maka abubuwanta da wasu mutane da take mu’amala da su. Ranar duk da tsautsayi ya sa ka binciko, za ka ji zuciyarka kamar za ta buga, saboda tsanannin mamaki. Daga nan ma wataƙila auren sai ya gutsure. Ka rabu da ita, wataƙila ma kuna da yara a tsakani. Ba sai na yi maka dogon bayani a kan matsalar rabuwa da mace mai ‘ya’ya ba.

Haka hana ta mu’amala da nesanta ta da ‘yan’uwa ta na jini. Kai kanka ka san ka taro Dala da Gwauron dutse da faɗin kai. Ba za ta taɓa yi maka biyayya ba a kan haka.

Sannan yanke mata alaƙa da mutane yana kawo mata tunani da rashin walwala har a kai ga cutar damuwa (depression). Kai ba ka nan, kuma ka ƙi bari ta mu’amalanci kowa. Wataƙila gida ita kaɗai. Kuma idan kana nan ba ka saurarenta. Ko kuma ita tana tsoron hira da kai ta gaya maka damuwarta saboda tana tsoronka. Kuma sam babu yarda a tsakaninka da ita.

Kuma ka sani Yayana, ba fa a yi wa mace dole a biyayya. Ba ‘yarka ba ce. Ka barta ta bi ka saboda Allah, da kuma kyautatawa. Ko ba ka ce ba, idan tana jin daɗin zama da kai za ta bi ka, ko ba ka tursasa ta ba.

Haka ƙuntata mace yana sa watarana ta yi maka bore. Kawai ɗabi’ar mutane ce. Ko yaya ka zafafa wajen ƙuntata mutum har ya kai bango, to watarana dole zai bijire maka. Ko da kuwa ɗanka na cikinka ne.

Haka zai rasa ƙimarsa a idonta don yana nuna mata rashin yarda da son kai, da kuma rashin adalci. Komai za ta yi masa sai dai don tsoron hukuncinsa ba wai don ƙauna da girmamawa ba. Ita yarda tana nuna so. Idan namiji yana kulle mace bai yarda da ita ba. Don haka ba maganar so. Haka idan mace tana sonka, za ta yarda da kai ko da ba ka tursasa ta ba.

Batun sana’a, ka hana mace neman na kanta ta yaya za ta kula da iyayenta da danginta? Ba a ce dole ne barin mace sana’a ba. Amma kyautatawa ce. Kuma ƙaruwar dukkanku ku biyun ce. Ka sani, idan mace tana sana’a, galibi ku]in akan yaranku yake ƙarewa da gidanku. Ɗan abinda take yafa wa iyaye da dangi kaɗan ne. Idan dai ba wata matsalar ce da ita ba, musamman ta rashin kamun kai ba, to bai kamata ka tauye ta ba. Domin duk abin taimakon juna ne. Don haka kulle ba ya saya maka so ko biyayyarta, illa lalata alaƙarku da ta’azzarar da rashin yarda a tsakaninku.

Ina godiya ga masu yi min fatan alkhairi da addu’a har ma da tsokaci da shawarwari. Na gode. Haƙiƙa shawarwarinku suna ƙarfafa min gwiwa. Allah ya kai mu mako mai zuwa.