Jami’an tsaro sun gano gawar da aka jefa cikin masai a Haɗejia

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse

Wani magidanci da ke garin Haɗejia mazaunin Unguwar Kwarin Manu ya sanar da jami’an tsaro dake aiki da rundunar Civil Defense cewar yana jin wari nai tsananin gaske a masan sa, lamarin da ya sa jami’an tsaron ba su yi ƙasa a gwiwa ba suka garzaya gidansa domin ba shi gudunmawar da yake buƙata.

Zuwan su gidan mutumin mai suna Umar Muhd mai shekara 47 ke da wuya sai suka farke masai ɗin da yake masu bayanin yana jin wancan wari marar iyaka, bu]e masan ke da wuya sai suka ci karo da gawar wata jaririya an lulluɓe a acikin wata rigar filo harta fara lalacewa, lamarin da ya sa suka garzaya da gawar zuwa babban asibitin Haɗejia domin likitoci su tabbatar da rayuwar jaririyar, lamarin da likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

Tabbatar da mutuwarta jaririyar da likitoci suka yi a babban asibitin na Haɗejia ya sa jami’an tsaron suka yi awon gaba da wanda ya kawo ƙorafin, wato Umar Muhd da nufin zurfafa bincike akan su, al’amarin domin zai taimaka masu wajen gano wanda ke da hannu wajen aikata waccan ta’asar.

Yayin da kuma hukumar tsaron ta miƙa gawar jaririyar a hannun mai unguwar Manu Kwari, Malam Musa Umar da jami’an ƙaramar hukumar Hadejia domin binne gawar kamar yadda addinin Musulunci ya yi tanadi.

Kakakin hukumar tsaro ta farin kaya, Malam Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni suka sakaya wanda ya gabatar da ƙorafin a ofishinsu, kuma suna ci gaba da bincike da zarar sun gano wanda ke da hannu anciki za su gurfanar da shi a gaban sharia. Don haka ya zama darasi ga masu sha’awar aikata irin haka nan gaba.