Gwamna Raɗɗa ya duba aikin gina makaranta ta musamman a Jiƙamshi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kai ziyarar duba aikin gina makaranta ta musamman (Special School) a garin Jiƙamshi, ƙaramar hukumar Musawa.

Makarantar na daga cikin guda uku da gwamnati ke ginawa a kowace shiyya ta jihar, domin bai wa ɗalibai masu basira (gifted) marasa galihu damar samun ingantaccen ilimi da zai bunƙasa hazaƙarsu.

Sauran makarantun akwai ta garin Raɗɗa a shiyyar Katsina wacce ake daf da ƙaddamar wa, da kuma ta Dumurƙul a shiyyar Daura, wacce ita ma tuni aikin yayi nisa.

By ukarofi