Jam’iyyar APC a Zamfara ta faɗa mummunan rikicin cikin gida

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jam’iyyar APC a Jihar Zamfara ta faɗa mummunan rikicin cikin gida biyo komawar Gwamna Dauda Lawal Jam’iyyar, yayin da ƙaramin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle ya koka kan abunda ya kira yin watsi da shi a siyasance.

Matawalle yayi wannan tsokaci a wata hirar wayar tarho da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta.

Matawalle ya koka bisa yanda Gwamna Dauda Lawal yaƙi tuntuɓar sa tun bayan komawar sa APC dangane da makomar jam’iyyar da rabon muƙamai a jam’iyyar kafin a gudanar da taron APC a Jihar.

Idan za a iya tunawa, jam’iyyar ta ƙasa ta fitar da jadawalin taron ta na jihohin Adamawa da Zamfara bisa umarnin su gudanar da taro a ranar takwas ga wannan wata na Afrilu amma abun yaci tura a Jihar Zamfara saboda rikicin cikin gida da ya addabi jam’iyyar ta APC.

Matawalle ya koka bisa yanda tsohon Gwamna Kuma Sanata Abdulaziz Yari yayi babakere game da sha’anin rabon muƙamai a jam’iyyar ta APC gabanin zaɓen Sabbin shugabannin jam’iyyar.

Wakilin mu ya ruwaito cewar jam’iyyar ta sanya yau Laraba 22 gaa wannan wata na Afrilu amma alamu sun nuna rikicin ya hana gudanar da taron a Jihar.

A cewar Matawalle, ya koka bisa yanda tsohon Gwamna Kuma Sanata Abdulaziz Yari yake neman ya tarwatsa Jam’iyyar don bukatun kansa.

“Tun bayan komawar Gwamna Dauda Lawal Jam’iyyar APC, Ina goyon bayan sa tsakani da Allah, amma abun damuwata shine, har yanzu Gwamna Dauda bai tuntube ni ba game da zaɓen Sabbin Shugabannin Jam’iyyar amma ya tuntubi Abdulaziz Yari.

Matawalle yayi nuni da cewar Gwamnatin! Dauda Lawal yayi hattara da Sanata Abdulaziz Yari, Yana Mai jaddada cewa za a ci amanar shi nan gaba a siyasar dake tafe.

By ukarofi