
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Laraba ne Shugaba Bola Tinubu ya karɓi baƙuncin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Saidai babu wani cikakken bayani a game da abin da ganawar tasu ta ƙunsa a yayin haɗa wannan rahoto.
Jonathan dai shi ne shugaban Nijeriya daga shekarar 2010 zuwa 2015.
Sunansa ya ƙara ƙarfi ne a 2015 a lokacin da ya karɓi kaye a zaɓen shugaban ƙasa da tsohon shugaban ƙasa marigayi Muhammadu Buhari ya doke shi a kai, lamarin da kuma ya sa ya zama shugaban Nijeriya na farko da yake rasa damar koma wa kujerar mulki, kuma ya miƙa ragamar jagorancin ƙasar cikin lumana.
