Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya naɗa Malik Anas a matsayin kwamishinan kasafin kuɗi da tsare tsare tare da sauya wa wasu wajen aiki.
Kafin muƙamin sa a matsayin kwamishina, Malik Anas shine mai baiwa Gwamna Shawara kan harkokin kuɗi,ya kuma taɓa riƙe muƙamin babban Akanta na jihar.
Anas yayi karatun digiri na biyu akan gudanar da kasuwanci (MBA) daga jami’ar Bayero da ke Kano.
Sanarwar ta fito daga babban sakataren yaɗa labarai na gwamna Malam Kula Muhammad sannan ya bayyana sauran kwamishinonin da aka canza wa wurin aiki.
Kwamishinan kasafin kuɗi da tsare tsare Alhaji Bello Hussaini Kagara da ya koma ma’aikatar kuɗi, Bashir Tanimu Gambo daga ma’aikatan kuɗi zuwa ma’aikatan kula da ƙananan hukumomi da masarautu.
Haka kuma Yusuf Rabi’u Jirdade daga ma’aikatar ayyuka na musamman zuwa ma’aikatar Kasuwanci, sai Adnan Nahabu daga ma’aikatar ciniki da masana’antu zuwa ayyuka na musamman.
Gwamna Dikko Raɗɗa ya kuma umurce Kwamishinonin da aka sauya wa wurin aiki da su cigaba da ayyukan su ba tare da ɓata lokaci ba.
