Gwamna Raɗɗa ya sa hannu kan sabuwar dokar kayan nauyi

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Dokar dai ta shafi saye da sayar da ƙarafan(kayan nauyi) a faɗin jihar.

Dokar ba ta haramta sana’ar ba ne,za ta gyara harkar ne ta hanyar tsabtacewa,ingantawa da samar da tsare tsare da za su gudanar domin amfanin al’ummar jihar.

Kamar yadda kundin dokar ya ƙunsa kuma aka raba wa manema labarai,duk masu wannan harkar za suyi rajista,kuma su sami lasisi daga gwamnati.

Haka kuma duk wani cinikayya da za ayi ,sai an rubuta sunan mai sayarwa , abinda aka sayar,rana da lokaci da kuma inda aka samo shi.

Duk harkar saye da sayar wa za ayi ta ne da rana a lokacin da aka ƙayyade ba da dare ba.

Kuma yara yan ƙasa da shekaru 18 ba za su saya ko sayar da kayan nauyi ba.

Dokar ta kuma tanadi cewa sai dillalai masu rajista ne kaɗai za su yi harkar a shagunan su ko ofisoshin su,ba sauran saye da sayar wa a wajen waɗannan wurare.

Ana sa ran wannan sabuwar doka za ta yi maganin matsalolin da ke tasowa a hidimar kamar sata da ɓarnatar da kayan gwamnati da sunan kwanan bola.

By ukarofi