Tsohon gwamnan Taraba ne ya buƙaci na tsere wa EFCC – Shaida

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Wani shaidar farko na hukumar EFCC, Ismail Lawal, ya shaida wa babbar kotun tarayya da ke Maitama, Abuja, cewa tsohon gwamnan Jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku, ya buƙace shi da ya tsere na tsawon watanni shida kada ya bayyana gaban hukumar EFCC domin amsa tambayoyi game da binciken da ake yi a kansa. Ishaku da wani tsohon sakataren dindindin, Bello Yero, na fuskantar shari’a kan zargin wawure kudin jama’a da suka kai Naira biliyan 27.

A yayin amsa tambayoyi daga lauyan tsohon gwamnan, P.H. Ogbole (SAN), Lawal ya bayyana cewa yana shirin bayyana gaban EFCC ne sai Ishaku ya hana shi, inda ya ce ya tsaya na watanni shida kafin a kama shi. “Na tambaye shi har nawa zan tsaya, ya ce watanni shida. Amma mutane sun riga ni sun je sun ba da bayanai a kaina, sun ce sun bani kuɗi, don haka idan EFCC ta gayyace ni kuma ban je ba, za su ɗauka cewa ni ne na ɗauki kudin,” in ji Lawal.

Ya kuma bayyana cewa ya kwashe kwana 40 a tsare a hukumar EFCC saboda ya kasa cika sharuɗɗan beli, duk da cewa ya fara bayar da bayani tun rana ta biyu ko ta uku bayan kama shi. Ya ce ba shi da masaniya ko ayyukan da aka ɗora masa sun kasance bisa ƙa’ida ko a’a. “Na dai je na karbo kuɗi daga inda aka ce in je, in bi umarni. Da na san cewa haramtaccen aiki ne, da ban je ba.”

A ƙarshe, Lawal ya bayyana cewa bai taba samun tabbacin cewa za a yi amfani da shi a matsayin shaida ba har sai da ya karanta a jarida. “Bayan haka ne EFCC ta sanar da ni cewa za su yi amfani da ni a matsayin shaida. Na amsa tambayoyi, an nuna min takardu, na ba da amsa a kansu.” Alƙalin kotu, Mai shari’a S.C. Oriji, ya ɗaga sauraren ƙarar zuwa 30 ga Satumba, 15 da 20 ga Oktoba, da kuma 6 ga Nuwamba 2025 domin ci gaba da shari’a.

By ukarofi