Daga USMAN KAROFI a Abuja
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da dakatar da shigo da tsoffin kayan aiki (scrap) daga yankin Arewa maso Gabas na Najeriya bayan fashewar wani abu da ya yi sanadin mutuwar ma’aikata 15 a wani wurin tara tsoffin kaya da ke Gidan Ƙarfe, kusa da Eastern Bypass a Kano. Wannan hukunci ya fito ne daga kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Kano, Ibrahim Umaru, a wata ganawa da Shugabannin Ƙungiyar ‘Yan Tsoffin Kaya ta Najeriya.
Kwamishinan ya bayyana cewa bincike ya nuna fashewar ta samo asali ne daga na’urorin fashewa da aka shigo da su daga Arewa maso Gabas ba tare da sani ba. Ya ce tun da yankin na fama da rikicin Boko Haram, akwai yiyuwar wasu ‘yan kasuwa na dauko irin waɗannan kayan cikin ganganci ko ba tare da an gane hakan ba.
A cewarsa, gwamnati za ta haɗa gwiwa da hukumomi domin sanya ido sosai kan irin waɗannan kaya da ke shiga jihar, don kare rayuka da dukiyoyin al’umma. “Dole ne mu ɗauki mataki don hana irin wannan bala’i faruwa a nan gaba,” in ji kwamishinan.
Shugaban ƙungiyar ‘yan tsoffin kaya ta Arewa, Alhaji Aminu Hassan, ya nuna goyon baya ga wannan matakin, tare da buƙatar a horas da ‘ya’yan ƙungiyar domin su riƙa gane kayan da ke da haɗari. Ya ƙara da cewa ƙungiyar ta bayar da umarni na dakatar da shigo da kowanne irin tsohon kaya daga yankunan da rikici ya addaba.
