Gwamnatin Kano ta haramta shigo da kayayyakin gwangwan jihar

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da haramta shigo da kayayyakin gwangwan daga yankin Arewa maso Gabas zuwa cikin jihar, a wani mataki na daƙile barazanar tsaro da ke ƙara ta’azzara a baya-bayan nan.

Kwamishinan tsaro na jihar Kano, AVM Ibrahim Umaru (mai ritaya), ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Ya ce matakin ya zama dole ne biyo bayan wasu fashe-fashe da suka faru a jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar tare da jikkatar wasu da dama.

A cewarsa, binciken da hukumomi suka gudanar ya nuna cewa bama-baman da suka tashi a cikin Kano, an shigo da su ne cikin kayayyakin gwangwan daga Arewa maso Gabas, yanki da ke fama da rikicin Boko Haram tun shekaru da dama.

Kwamishinan ya jaddada cewa wannan mataki na gwamnati na da nufin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da daƙile duk wata barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

Ya kuma gargaɗi ƴan kasuwa da masu safarar irin waɗannan kayayyaki da su kiyaye dokar, yana mai cewa duk wanda aka samu da karya ta, zai fuskanci hukunci mai tsanani.

By ukarofi