Yanzu-yanzu: Tsohon golan Super Eagles, Peter Rufai ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon mai tsaron raga na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles, Peter Rufai ya rasu bayan shafe shekaru 61 a duniya.

A sanarwar da Super Eagles ta wallafa a shafinta na X, ta ce tsohon ɗan wasan yana ɗaya daga cikin tawagar ƴan wasan da ta lashe kofin gasar ƙasashen Afirka, wato AFCON a shekarar 1994.

Ta kuma bayyana jimaminta game da rashin ɗan wasan, wanda ta ce za a cigaba da tunawa a sakamakon kyawawan halayensa.

A ranar Alhamis ne Rufai, wanda ake kira da ‘Dodomayana’ ya rasu bayan fama da wani rashin lafiya.

Haka kuma yana cikin ƴan wasa na farko da suka wakilci Najeriya a Kofin Duniya na 1994 a Amurka.

Ya kuma sake buga wa Super Eagles gasar da aka yi a ƙasar Faransa a shekara ta 1998, lamarin da ya kai jimillar wasanni 65 da ya buga wa ƙungiyar.

Hakan na zuwa ne sa’o’i bayan rasuwar ɗan wasa Diogo Jota na ƙungiyar Liverpool bayan shafe shekaru 28 a duniya.

Ɗan wasan, wanda ɗan asalin ƙasar Portugal ne, ya rasu ne tare da ɗan uwansa makonni biyu da aurensa, a wani hatsarin mota da suka yi a garin Zamora dake ƙasar Sifaniya.

By Babaji